Daga Awwal Umar Kontagora An bayyana cewar biyan kudin hadaya ga maniyyatan Neja da gwamna Umar Bago ya yi abin a yaba ne. Domin...
Daga Awwal Umar Kontagora
An bayyana cewar biyan kudin hadaya ga maniyyatan Neja da gwamna Umar Bago ya yi abin a yaba ne. Domin wannan ya nuna cewar gwamna ya damu da halin da maniyyatan Neja ke ciki.
Shugaban ƙungiyar Hajji and Umrah Trainers a jihar Neja, Sheikh Liman Muhammad Masha'Allahu ne ya bayyana hakan a wata takardar manema labarai da ya fitar yammacin Alhamis din makon nan a Minna.
Masha'Allahu, ya ci gaba da cewar duk da tsadar kudin kujerar hajji ta bana bai mahajjata sun samu wani guzurin kirki ba, wanda idan an ce a cikin kudin Alhaji zai yi hidimar Ibadah kuma yaci abinci a ciki tabbas zai ta gayyara, amma wannan matakin na gwamna Umar Mohammed Bago na baiwa mahajjata tallafin kudin hadaya abin a yaba ne wanda ya zama wajibi masu hali da su yi koyi da irin wannan matakin na tausayawa musamman ga talakawan da suke zaune da su.
Yana da kyau, masu hali da su ji tsoron Allah su tausaya da dan abinda ke hannunsu wajen tallafawa marasa karfi musamman a wannan lokacin hidimar sallar.
Malamin, yace a wannan yanayin yana da muhimmancin gaske mu tausayawa junan mu, wanda ya samu damar lahiyya ya samma wadanda ba su samu dama, kuma bai zama wajibi ka jefa kan ka cikin yanayin da baka da halinsa, domin cin bashi dan hidimar sallah babbar kuskure ne, amma idan kana da hali kuma yana da kyau ka kyautatawa iyalan ka, kai ma za ka samu natsuwa da jin dadi idan ka ga iyalan ka cikin walwala.
Shehin malamin ya nemi maniyyata da ke kasar mai tsalki da su yi anfani da wannan damar wajen yiwa gwamna Umar Bago addu'o'in samun nasara da jihar Neja akan matsalar tsaro da ya addabi wasu sassan jihar, da kasar mu Nijeriya da kuma shugabannin mu wajen samun kwazo da kwarin guiwar gina jihar da kasar musamman arewacin kasar nan da ke fama da matsalar tsaro.
Masha'Allahu, ya nemi masu da su rige-rige wajen ayyukan alheri na taimako da jinkai ga marasa karfi dan samun kusanci ga Allah ( S.W.A).
Malamin, ya ce muna fata da rikon Allah da ya baiwa wadanda hakkin biyan kudaden kujerun hajji damar sanin kurakuran da su kayi na tsadanta kudin kujera wanda saukakawar zai baiwa al'ummar musulmi damar samun kwarin guiwar shiryawa shekara mai zuwa ta yadda maniyyata ba zasu shiga cikin matsi ba.
No comments