Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dole Mu Koma Ga Allah Sannan Mu Iya Cin Moriyar Tsarin Dimukuradiyya - Amb. Musa

Daga Awwal Umar Kontagora Shugaban kungiyar Mahaddata Alkur'ani mai tsarki da makarantun Tsangayu reshen arewa ta tsakiya, A...

Daga Awwal Umar Kontagora

Shugaban kungiyar Mahaddata Alkur'ani mai tsarki da makarantun Tsangayu reshen arewa ta tsakiya, Amb. Musa Adamu ya ce maganganun kushe da zage zagen da jama'a ke yi kan rashin cigaba a tsarin dimukuradiyyar kasar nan, ba shi ne mafita ba, face kowa ya koma ya dubi kurakuransa ya gyara sannan tsarin shugabancin mu zai samu alkibla.

Amb. Musa Adamu, ya bayyana hakan ne lokacin da yake fadin ra'ayinsa ga manema labarai dangane da bukin ranar talatar makon nan da muke ciki.

Ambasada, ya cigaba da cewar ya kamata shugabannin mu na siyasa su san dalilin da yasa talaka ya zabe, shi ma talaka ya kamata kwakkwaran dalilin da yasa yake yin zabe, wanda dole mu fita cikin wannan duhun kafin mu san irin mutanen da za mu rika zaba.

Amma maganar zagi ko sukar gwamnati da jama'a ke yi ba zai anfanar ba, domin wadanda muke zaba a cikin mu suke kuma yan uwan mu da muke fadi tashi tare amma bayan tafiyarsu kan kujerun sai su manta da abinda su ka tafi aiwatarwa, saboda haka wajibi ne mu ilmantar da junan mu ko a gaba idan zabe ya taho mu san irin mutanen da za mu rika zaba.

Tsarin dimokuraÉ—iyya tsari ne da ya bai wa al'umma damar zaben wadanda za su shugabance su, amma shugabancin akan wace manufa kuma  me zasu aiwatar idan sun tafi kan kujeran da su ka tafi wakilcin, amma muna zabe ne a makance kuma muna zaben mutanen da zasu karkatar da abinda aka ba su dan yiwa kasa aiki, saboda haka dole idan muna son a gaba siyasar tayi kyau idan irin wannan ranar tazo mu samu abin nunawa.

Dan haka ina kira ga talakawa da su bude idanu su fahimci irin kurakuran da suka aikata a baya da su gyara tafiyar gaba. Amma maganar suka ko zagi ba shi mafita ba face gyara kuskuren da muke yi a lokacin zabe, domin ita siyasa hanya ce ta shugabanci bisa kyautatawa al'umma, aiki tukuru dan cigaban kasa, domin Alkur'ani mai tsalki ya fayyace komai akan shugabanci, kuma abin tambaya ne gobe a gaban Allah.

Ina bai wa al'umma shawara maimakon suka ko zagi ga shugabanni mu mayar da komai ga Allah mu taimaka masu da addu'o'i, domin idan mun tsine suka lalace mune za mu cigaba da fuskantar wannan yanayin da muke ciki.

Kuma, da yardar Allah idan muka gyara wajen zabe a gaba, zamu samu shugabanci mai inganci kuma a shekarar gaba ba gwamnati ce za ta bayyana mana ayyukan da tayi ba, mu ne za mu fadawa duniya nasarorin da gwamnatin ta samu.

No comments