Da Awwal Umar Kontagora An bayyana cewar gaggauta shelar hana hawan sallah da jami'an tsaro su ka yi a jihar Kano, sun kyaut...
Da Awwal Umar Kontagora
An bayyana cewar gaggauta shelar hana hawan sallah da jami'an tsaro su ka yi a jihar Kano, sun kyautawa Kanawa, domin yunƙuri ne na hana haifar da kwantaciyyar fitina da wasu ke ƙoƙarin haddasawa.
Alhaji Shu'aibu Bichi wani haifaffen Bichin jihar Kano ya bayyana ma wakilinmu hakan a wata tattaunawarsu ta wayar tarho a yammacin ranar Alhamis.
Bichi, ya ci gaba da cewar gwamnatin ta wuce ta rusa masarauta, wannan gwamnatin da ta zo ita ma rusa waccar masarautar, to tunda akwai hurumin zuwa kotu kuma kotu ta tabbatar tana da hurumin sauraren ƙarar a ba ta dama tai aikinta, duk ɓangaren da kotu ta ce ita ce halastacciya sai ɗayan ɓangare ta yi haƙuri.
Amma maganar yin hawan sallah a wannan lokacin kowa shaida ne yunƙuri ne na tada fitinar da ke bacci, gaskiya na yabawa rundunar yan sanda na daukar wannan matakin domin mataki ne da zai samar da zaman lafiya a jihar Kano.
Saboda haka ina kara baiwa rundunar yan sanda shawara da su kara kaimi duk wani abinda zai kawo fitina su gaggauta kawar da shi, mu a jihar Kano duniya ta shaidi jihar zaman lafiya ne, ba kuma za mu goyi bayan hada kan yayan jihar Kano dan cin ma wata boyayyar manufa ba.
Alhaji Shu'aibu Bichi, ya yi kira ga al'ummar jihar Kano da su ajiye maganar bambancin siyasa a gefe duk da cewar gwamnatin da ta shude tayi kokarin haddasa rashin fahimtar juna ga Kanawa, mu tabbatar mun sanya jihar Kano gaba don ita ce cibiyar cigaban ƙasar nan, kuma da zarar mun bai wa maƙiya dama lallai mu tabbatar ba jihar Kano ba gaba ɗayan arewa ta samu matsala, In ji shi.
No comments