Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Burina Shi Ne Na Taimaka Wa Mata Ƴan Uwana, In ji Garkuwar Matan Giwa

Daga Idris Umar, Zariya Hajiya Zainab Sani, Giwa ta zama Garkuwan matan Giwa dake ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna. A lokaci...


Daga Idris Umar, Zariya

Hajiya Zainab Sani, Giwa ta zama Garkuwan matan Giwa dake ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

A lokacin da take zantawa da manema labarai a gidanta dake garin na Giwa Hajiyar ta nuna jin daɗinta da Allah akan karamci da ƙasar Zazzau ta nuna mata na ba ta matsayi na garkuwar matan Giwa .

Hajiya Zainab ta ƙara da cewa hakan ya ƙara mata ƙwarin guiwar taimakawa mata kamar yadda ta saba yi a tsawon rayuwarta. "Domin taimakawa mata shi ne burina a rayuwata", a cewar ta. 

Kuma Hajiyar ta yi yabo ga Sarkin Zazzau  Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli bisa gudummawa da yake ba su a ƙungiyar su ta matan Musulmi (FOMWAN) kuma ta yabawa Hakiminta Uban Doman Zazzau da shugaban ƙaramar hukumar Giwa, Honorabul Abubakar Shehu Kawal Giwa da ƙungiyoyin da suke bai wa mata tallafi da 'yan majalisar su bisa taimako da suke bai wa mata da marayu da suke ƙaramar hukumar ta Giwa da sauran wurare baki ɗaya.

Ƙarshe ta jinjinna wa mijinta bisa bata goyan baya da yake yi dare da rana ta ce Allah ya saka mishi da alkhairi.

Hajiya Zainab dai ta zama Garkuwan mata lokaci guda kuma ita ce shugaban mata musulmi a shiyyar Ikara da Birnin Gwari har da ƙaramar hukumar Kudan kuma bincike ya nuna cewa tana riƙe da muƙamai masu yawan gaske bisa irin jajircewarta a harkokin taimakawa mata da marayu a jihar Kaduna.

Hakan yasa ta yi kira ga iyaye da su ƙauracewa ɗorawa yara ƙanana talla maimakon haka a tura su makaranta Islamiyya da Boko.

Ta ce ta nemi masu hannu da shuni da su rinƙa sanya dukiyarsu wajen taimakawa marayu, ta ce hakan zai rage ƙalubalen da yara ƙanana ke fuskanta a rayuwarsu musamman marayu.

Mata da yawa suke murna da karamcin da Hajiya Zainab ta samu a matsayin Garkuwar su ta matan ƙaramar Hukumar  Giwa a cikinsu harda Malama Sumayya Sa'adu, Funtua ɗaliba a Fudiyya Islamic School Samarun Zariya.

No comments