Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mazhabar Malikiya Azumin Gobe Asabar Wanda Ya Yi Daidai Da Arafat Ingantacce Ne - Barr. Maidala'ilu

Daga Awwal Umar Kontagora Babban limamin masallacin juma'ar Tunga da ke cikin garin minna, Barr. Muhammad Salisu Maidala...


Daga Awwal Umar Kontagora

Babban limamin masallacin juma'ar Tunga da ke cikin garin minna, Barr. Muhammad Salisu Maidala'ilu ya bayyana cewar takaddamar da ake yi kan ingancin azumin gobe asabar wanda yayi daidai da ranar Arafat halas ne, domin hadisin ma malamai sun tabbatar da rashin ingancin shi.

A cewarsa koda ma hadisin ya inganta mu a mazhabar malikiya, yin azumin gobe asabar halas ne domin ba azumin asabar mutum yayi niyya ba azumi ne da yayi daidai da ranar arafat.

Malamin ya bayyana hakan ne a hudubar juma'ar makon nan,inda yayi karin haske da cewar kamar yadda ya inganta yin azumin ranar arafat ana kan kare zunuban mutum na shekarar da ya gabata zuwa wata shekarar,  ka ga an kwadaitar da mu wannan azumin bai kamata musulmi ya bari a bar shi a baya ba dan kwadayin wannan ruhusar, domin a wannan ranar Allah yana kasancewa bayinsa kuma hakan ne yasa aka kwadaitar da mumini da ya guji aikata ash-sha a ranaku uku na bayan arafat, domin Allah na yin kyautar gafararsa ga bayinsa.

Idan aka kwatanta daren lailatul kadari wanda ya tsaya a wannan daren ne wanda mala'ikun Allah ke sauka a cikin shi, shi kuma ranar arafat Allah ne da kan shi yake daidatuwa tare da bayinsa a wannan yinin ka ga ke nan akwai bukatar kwadaitar da bayin Allah muhimmancin wannan rana.
Limamin ya cigaba da cewar a kwanaki ukun bayan arafat ana son mutum ya yawaita salatin annabi da sauran azkarorin da suka inganta daga hadisan manzon Allah, ayyukan alheri domin Allah kan yi bonanza a wannan lokacin ga bayinsa muminai.

Malamin, ya jawo hankalin matasa kan fakewa da bukukuwan sallah wajen aikata alfasha, wanda a cewarsa wannan ba karamin hasara ba ne ga rayuwar mumini musulmi ya rasa abin yi a irin wannan lokacin muhimmanci da ya wuce aikata sabo ga mahaliccinsa. Iyaye da shugabanni da gwamnati ya kamata su sanya idanu a irin wannan lokacin idan an ga asar na barna da a tabbatar an dakatar da shi a cikin al'umma.

No comments