Daga A'isha Suleman Zariya Sarkin Dnata HRH Injiniya James Bitrus Abwaminajiya Sa'dnatayi na (l) ƙaramar hukumar Kagarko...
Daga A'isha Suleman Zariya
Sarkin Dnata HRH Injiniya James Bitrus Abwaminajiya Sa'dnatayi na (l) ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna ya mika saƙon fatan yin bukukuwan sallah lafiya a faɗin masarautar sa da jihar Kaduna baki ɗaya.
Sarkin wanda ya zanta da manema labarai a fadarsa dake cikin garin Tafa dake hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Sarkin ya ce, yana yi wa dukkanin al'ummar musulmi fatan alheri kuma ya yi addu'ar Allah yasa yadda za su fara lafiya su gama cikin aminci.
Da yake magana akan batun haÉ—in kai ya ce wajibi ne Musulmi da wanda ba Musulmi ba su haÉ—a kansu, inda ya ce yin hakan zai sanya a sami ci gaban juna kamar yadda iyaye da kakanni suka yi a lokacin baya.
A ƙarshe ya yi jinjina ga Limamai da Fastoci da ɓangarorin jami'an tsaro da suke aiki tare wanda hakan yasa zaman lafiya yake kara samuwa a ƙaramar hukumar Kagarko baki ɗaya
Ya ce da ikon Allah Musulmi za su yi bikin sallah lafiya. "ina taya su murna ni da dukkan jama'ata. Allah yasa a yi Sallah lafiya", in ji shi.
No comments