Daga Bello Hamza , Makkah A yayin da ake shirye shiryen fara aikin bana, Alhazai daga kananan hukumomi 44 na Jihar Kano sun nun...
A yayin da ake shirye shiryen fara aikin bana, Alhazai daga kananan hukumomi 44 na Jihar Kano sun nuna jin dadinsu da yabawa ga Gwamnan Jihar Kano a kan yadda ya bijiro da tsare-tsaren da suka sanya zaman su a garin Maddinah da Makkah ya zaman a daban, “Domin an kula da masaukai da abinci an kuma kula lafiyarsu yadda ya kamata”, wani shahararren Malamin addnin musulunci kuma shugaban masu ilimin Taurari na nahiyar Afirka gaba daya, Sheikh Muhajjadina Sani Kano, ya bayyana haka a tattaunawarsu da Wakilinmu a garin Makkah.
“Muna yaba wa da shirye-shiryen hukumar Alhazai ta Jihar Kano sun yi kokari tun daga gida har zuwa kasa mai tsarki, sun gudanar da bita-bita ga alhazan don su fahimci yadda za su gabatar da aikin hajji karbabiyya” in ji.
Ya kuma kara da cewa, “Hukumar ta samu nasarar shigo da dukkan alhazan jihar sai dai kawai wasu mutum biyar da suka samu lalurori daban-daban. An samu nasarar tafiya da dukkan alhazan zuwa garin Madinah, inda suka yi ziyarori daban-daban da kuma masauki da abinci cikin aminci. Babu wanda ya yi korafi, har kaji da nama da kifi ya fara ginsar alhazai. Wannan kuma kokari ne na Gwamnan Abba Kabiri Yusuf, don haka ina kira ga dukkan gwamnnonin Nijeriya har da shugaban kasa da su yi koyi da Gwamna Kabir a kan irin aikin alhairin da yake yi. “Shi ya sa zaka ga kusan dukkan alhazan suna masa addu’ar Allah ya taimaka masa”.
Idan za a iya tunawa, Gwamnan ya ba da tallafi na musamman ga alhazan jihar, donmin cika musu kudaden aikin zuwa hajji, haka kuma sai da ya tallafa wa alhazan a bangaren kudin guziri. A kan haka muna kira ga al’ummar Jihar Kano su ci gaba da ba gwamnatin Abba dukkan goyon da ya kama don a samu nasarar aiwatar da ayyukan raya kasa da bunkasa rayuwar al’ummar jihar gaba daya.
Daga karshe ya nemi hukumar alhazai su kara kaimi wajen inganta jin dadin rayuwar Alhazai ta hanyar samar musu da masaukai kusa da Harami.
No comments