Daga A'isha Suleiman Zariya Gwamnatin jihar Kaduna a ƙarƙashin jagorancin Sanata Uba Sani ta kula da almajirai kamar yadda m...
Daga A'isha Suleiman Zariya
Gwamnatin jihar Kaduna a ƙarƙashin jagorancin Sanata Uba Sani ta kula da almajirai kamar yadda mai bai wa gwamnan shawara a kan shirin ciyar da abinci a makarantu, Hajiya Fauziyya Buhari Adam, ta bayyana a yayin bikin babbar sallah wadda aka yi a ranar 16 ga watan Yunin shekarar 2024.
Hajiya Fauziyya Buhari Adam, a wata ziyara da ta kai a makarantar kwana ta almajirai a ranar babbar sallar mai suna Umaru Musa 'Yar Adua Almajirai Bilingual Model Primary School IQTE Sabon Gari, Marabar Gwanda da ke ƙaramar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna, ta bayyana cewa hakan ne ya sa ta shirya masu cin abincin sallah domin su ji cewa lallai gwamnati ta san da su.
Hajiya Fauziyya yayin da ta ke ƙarin haske a kan manufofin gwamnatin Uba Sani musamman a kan makarantun Tsangayu da kuma almajirai, ta nuna cewa za su cigaba da tallafawa makarantun kwana na almajirai a fadin jihar Kaduna da kuma ganin yadda za a zaburar da malamai da almajiran domin su zama mutane na gari da al'ummar jihar Kaduna baki daya.
"Muna da irin waɗannan makarantun guda takwas a Kaduna," a cewarta, inda ta bayyana cewa, "Makarantar nan an yi ta ne saboda almajirai, a arewa muna da almajirai da yawa, in muka bari abin ya taɓarɓare, ba a zo an kula ba, ba a sa ido a kansu ba, arewa za mu ci baya da yawa, to shi ya sa aka buɗe irin waɗannan makarantu. Muna da ita a Tudun Jirgi Soba, IQTE Mararrabar Gwanda, IQTE Labar, IQTE Jere, muna da su dai da yawa."
Mai bai wa gwamnan shawara, wadda ta bayyana yaran da waÉ—anda suka fi neman a taimaka masu, ta ce, "Iyayen yaran ba su da hali, suna ganin kamar ba su da gata, amma muna nuna masu cewa suna da gata, saboda mu kanmu mun bar iyalanmu mun zo domin mu zauna mu yi bukin sallah a tare da su." Kamar yadda ta bayyana a cikin dogon jawabi da amsa tambayoyi da ta yi da manema labaru.
Shugaban makarantar, Abdulhamid Aliyu, wanda ya bayyana cewa akwai kimanin dalubai 500 a makarantar, ya yi godiya ga gwamnatin jihar Kaduna a bisa canji da suka gani ta ɓangaren ciyarwa da kulawa, inda ya yi yabo ga Hajiya Fauziyya tare da bayyana cewa, "A bara wancan ta kawo mana raguna guda biyu, an ci raguna, an ci girki, an yiwa yara girki mai dadi, an yi addu'a, an yiwa jihar Kaduna addu'a da kasa baki daya addu'a, yau kuma gashi yau take sallah, ga shi tana tare da yara, ga rago an yankawa yara, ga girki ana yi, yara suna cikin annashuwa, fiye da yadda za su ji a gida." kamar yadda ya bayyana, sai ya yi addu'a ga gwamnatin jihar Kaduna.
Iyaye da dakaci da suka makarantar duk sun bayyana jin dadinsu da yadda gwamnatin jihar Kaduna ke kula da yaran da kuma iliminsu.
Jamilu Ahmad Ibrahim, É—aya daga cikin almajiran makarantar, ya bayyana jin dadinsa inda ya ce,"Allah Ya daukaka gwamnatin Uba Sani, ta bamu rago kwanaki ba ma sallah ba. Muna godiya, muna so ya dauki Hajiya Fauziyya ya kai ta matsayin da ya fi wannan." Sai ya bayyanawa manema labaru cewa akan ba su abinci, lemu (juice), "cake".
Shima Umar Muhammad almajiri ne a makarantar wanda ya zo daga Marabar Gwanda, almajirin godiya ya yi shima, inda ya ce, "Muna samun abinci a nan fiye da gida, Allah Ya kaita matsayi da ba ta taba tunani, Allah Ya taimaketa."
An kammala bikin sallar tare da almajiran cikin nasara.
No comments