Daga Awwal Umar Kontagora An yi kira ga shugabannin ɓangarorin APC da NNPP da su guji yin amfani da ƙudurin siyasa wajen cutar da Kano domin...
Daga Awwal Umar Kontagora
An yi kira ga shugabannin ɓangarorin APC da NNPP da su guji yin amfani da ƙudurin siyasa wajen cutar da Kano domin matsalar masarautar Kano matsala ce da ta shafi arewacin ƙasar nan ba jama'ar Kano kawai ba. Jigo a jam'iyyar APC kuma daya dattijai a arewacin kasar nan, Alhaji Hamza Yanga Buba ne yayi kiran a wani shirin gidan rediyo a safiyar Juma'ar nan a Minna.
Yanga Buba, ya ci gaba da cewar jihar Kano kusan itace cibiyar arewacin kasar nan, idan dattijan arewa suka cigaba da sanya idanu abin da ke faruwa yanzu ya cigaba, tabbas wannan rikicin ba zai haifar da da mai ido ba. Saboda haka akwai bikatar dukkanin bangarorin da ke rikici da juna da su ajiye son zuciyarsu a gefe daya, su dubi walwala da rayuwar al'umma domin kananan abubuwan da ke faruwa yanzu idan ba a samu maslaha ba wanda zai iya tabbatar ma da inda rikicin zai tsaya.
Dole ne Dr. Umar Abdullahi Ganduje na bangaren APC ya mayar da takobinsa kube, haka wajibi Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso ya mayar da gudumarsa makera, su yi abinda ya dace na zaman lafiya, domin turbar da suka hau gaba dayan su ba mai bullewa ba ce.
Arewa an gama gurgunta mu, Boko Haram a arewa ta samu gindin zama, Garkuwa da jama'a dan karban kudin fansa a arewa ta samu gindin zama wanda yayi sanadin dubban mutanen karkara suka zama yan gudun hijira, ya kamata in har suna son cigaban jihar Kano da aka shaide ta da zaman lafiya, kuma suna bukatar yar walwalar da talakawan arewa ke dan samu a yanzu su tabbatar sun gaggauta kawo karshen wannan rikicin, domin dukkaninsu yan asalin Kano kuma muna alfahari da su.
Dattijon yace lokaci yayo da dukkanin yan majalisun jahohi da na tarayya su tabbatar duk wani kudurin dokar da zasu gabatar ya zama kuduri ne da zai kawo hadin kai da cigaban tattalin arzikin kasa, amma idan za a cigaba da yin dokoki bisa son zuciya tabbas za a cigaba da samun koma baya a tsarin siyasar kasar nan.
Jihar Kano na da kananan hukumomi arba'in da hudu, kuma dukkan kananan hukumomin nan APC da NNPP na da magoya baya, idan ma.maganar rarraba masarauta ta tabbata tp a tabbatar an yi dokar da za ta yi rarrabon nan bisa adalci, sannan dukkan bangarorin Sanusi da Aminu suna da magoya baya a tabbatar an yi abinda ya dace dan samun zaman lafiya.
A karshe, dattijon ya yi kira ga gwamnonin arewacin kasar nan, da su ajiye maganar banbancin jam'iyya a gefe su dubi matsalar tsaron da kyau, idan har manoma ba su samu kariya daga yan ta'addar daji ba, mu tabbatar dawp da martabar sana'ar noma da kiwo da aka san mu akan shi zai zama tarihi. Wanda halin da muke ciki a yau kowa na ji a jikin shi saboda tsadar abinci da sauran kayan more rayuwa.
A samar da tsaro yadda ya dace, a samar da takin ga manoma da yardar Allah idan akai haka za a samu mafita a wannan yanayin da ake ciki yanzu.
No comments