Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Jami'an Tsaro Shida Na Cikin Mutanen Da Aka Kashe A Harin Katsina - Rahoto

Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Katsina ta ce akwai dakarunta huÉ—u da kuma dakarun tsaro biyu na gwamnatin jihar cikin mutanen...



Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Katsina ta ce akwai dakarunta huÉ—u da kuma dakarun tsaro biyu na gwamnatin jihar cikin mutanen da 'yanbindiga suka kashe a harin da suka kai ranar Lahadi.

Kakakin 'yansadan a Katsina, Abubakar Sadiq Aliyu, ya faɗa cikin wata sanarwa cewa an tsaurara tsaro a yankin ƙaramar hukumar Kankara, inda suke aiki da sauran hukumomin tsaro don kare sake aukuwar harin.

"A ranar 8 ga watan Yuni da misalin ƙarfe 3:00 na rana maharan suka far wa garuruwan Gidan Tofa da Dan Nakwabo, inda suka harbe mutum 20 tare da raunata wasu biyu, sannan suka yi wa motarmu mai silke kwanton ɓauna kuma suka kashe jami'an 'yansanda huɗu da kuma biyu cikin dakarun tsaron gwamnatin Katsina (KSCWC)," in ji sanarwar.

Tun da farko rahotonni sun ce aƙalla mutum 25 aka kashe a hare-haren sannan aka sace wasu da ba a san adadinsu ba.

An yi jana'izar wasu daga cikin mutanen da aka kashe yayin da jami'an tsaro ke ci gaba da laluba dazukan da ke kusa don ƙwato waɗanda aka sace.

No comments