Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kashe Mutum 50 A Katsina: Tinubu Ya Ce A Kamo Maharan

Shugaba Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su kamo maharan da suka kai hari a Æ™ananan hukumomin Dutsin-Ma da Kankara na jihar Katsina da ya y...


Shugaba Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su kamo maharan da suka kai hari a Æ™ananan hukumomin Dutsin-Ma da Kankara na jihar Katsina da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da tabbatar da an hukunta su.

Shugaban ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman Ajuri Ngelale ya fitar a ranar 11 ga watan Yuni, 2024 yana mai kakkausar suka kan yawaitar hare-hare a ƙasar.

A yayin da ya bayyana sabbin hare-haren a matsayin munanan hare-hare, shugaban ya jaddada cewa za a Æ™ara Æ™aimi wajen tabbatar da tsaron ‘yan kasa da kuma taarwatsa ‘yan ta’adda gaba daya da sauran masu tayar da zaune tsaye da kuma baÆ™in ciki a kowane É“angare na Æ™asar.

Shugaban ya jajantawa iyalan waÉ—anda abin ya shafa, da gwamnati da kuma al’ummar jihar Katsina, tare da addu’ar Allah ya jikan waÉ—anda suka rasu.

No comments