Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ma'aikata Fararen Hula Sun Yi Zanga-Zanga Kan Yadda Sojoji A Nijeriya Ke Muzgunawa Musu

Ma’ikata fararen hula da ke aiki a cibiyoyin da ma’aikatun tsaron sojojin Najeriya sun gudanar da wata zanga-zanga tare da rufe ma'aikat...



Ma’ikata fararen hula da ke aiki a cibiyoyin da ma’aikatun tsaron sojojin Najeriya sun gudanar da wata zanga-zanga tare da rufe ma'aikatar tsaron sojoji da ke Abuja a ranar Talata.

Ma’aikatan dai sun gudanar da wannan zanga-zangar ne bisa zargin da suke cewa sojoji na cin zarafin su, inda da dama daga cikin su ke ci gaba da zama a tsare a hannun sojoji.

Sun bayyana cewa jami’ai sojoji na Æ™untata musu ta hanyar dukan su da kuma kulle su a gadirum duk da cewa su fararen hula ne ba sojoji ba.

Masu zanga-zangar sun kuma bayar da misali da wani mai suna Ambrose Akhigbe wanda mataimakin darakta ne a makarantar sakandiren ‘ya’yan sojoji da ke jihar Legas da wani jami’in soji ya azabtar da shi a ranar Litinin ba tare da la’akari da dokokin da suka shafi ma’aikatan gwamnati fararen hula ba.

Bayan aukuwar wannan zanga-zanga ta wadannan ma’aikatan, Dakta Ibrahim Abubakar Kana babban sakatare a ma’aikatar tsaron Najeriya ya yi wa ma’akatan jawabi, inda a ciki ya sanar da su cewa za a duba wannan korafi nasu.

Ya tabbatar da cewa za a gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar lamarin. Ya kuma ce sun sa na kama dukan wdanda ake zargi da hannu a cin zarafin ma’aikata fararen hulha da ke cibiyoyin tsaron Najeriya.

An dade ana bayyana cewa jami’na sojoji na yi ma ma’aikta fararen hulha gwale-gwale tare irin na soji, a duk lokacin da wani abu ya faru tsakaninsu, sai dai wannan shi ne ne kusan karo na farko da aka samu sun fito sun bayyana damuwarsu a fili.

No comments