Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Matashi Na Farko Da Ya Zama Memba A Ƙungiyar FIFA Ya Nusar Da Matasa Kan Muhimmancin Wasanni Motsa Jiki

Daga Awwal Umar Kontagora Abdullahi Abubakar Mokwa, shi ne matashi na farko da ya zama mamba a kungiyar FIFA ta kasa, ya nemi ma...


Daga Awwal Umar Kontagora

Abdullahi Abubakar Mokwa, shi ne matashi na farko da ya zama mamba a kungiyar FIFA ta kasa, ya nemi matasa da su rungumi wasanni motsa jiki zai taimaka masu wajen sanin muhimmancin rayuwarsu da kwarewa wajen taimakawa rayuwarsu ta hanyar cudanya da al'umma.

Matashin ya ce shi a kashin kan shi ya taimakawa matasa da dama sama da ashirin ta hanyar yi masu rajista da taimaka masu da kayan motsa jiki.
Yace bangaren wasanni na karawa mutum kwazo wajen dogaro da kai da kaucewa shiga cikin miyagun dabi'u da ke jifa matasa cikin harkar shaye shaye da zama bata gari cikin al'umma.

Matashin ya ce wannan matsayin ya same shi ne bisa kokarinsa da gogewa wanda ba zai iya mantawa da gudunmawar da Coch Bala Fresh ya ba shi ba, wanda shigar sa FIFA ya fahimci duniya ta karkata ne akan matasa domin yanzu lokacin tsoffi ya wuce matasa ne duniya ke yayi, idan matasa ba su natsu sun taimaki kan su ba, ba wani jigo ko jagora da zai yi sha'awar tafiya da su a kowace harka ba, lallai zama mai hura wasa ko sanya idanu akan yadda harkokin wasanni ke gudana dole sai ka zama natsattse wato kamili da zai iya zama wani abu a harkar wasa ba.

Saboda haka maganar banga, ko daba ba dabi'a ba ce da kai mutum nasara a rayuwa ba, ya zama wajibi mu jawo hankalin matasa yan uwan mu da su ajiye duk wani tunani marar kyau, su rungumi dogaro da kai, su samarwa kan su mafitar da za a yi na'am da su.

Ina mai jawo hankalin sauran sassan jiha musamman manyan kananan hukumomin jihar nan, kamar su Kontagora, Suleja, Bida da Chanchaga da su zama abin misali wajen karfafa yara masu tasowa tun daga matakin faramare, zuwa sakandare wajen daukar nauyin tallafawa masu kwazo, domin idan ka taimaki matashi daya a harkar cigaba ka tallafawa al'umma da dama ne.

Yau muna kallon wasan Badmiton da wasu masu kishi suka assasa kuma na fahimci muna da hazikai da in sun samu kulawa za su iya zama wani abu da duniya za tayi alfahari da su bada jimawa ba, akwai hucky, akwai takwando akwai wasanni polo duk wasanni ne da aka san jihar nan tayi shuhura akan su a baya, amma rashin kulawa yasa muka yi baya sosai.

Mun sani a baya da wadannan wasannin akwai wadanda suka zama wani a yau da duniya ke tutiya da su a bangarori da dama, amma bayan sun samu irin wannan damar su me suka yi na nuna kishin inda suka fito.

Ya zama wajibi mu farka daga dogon baccin da muka yi, kowa ya yi tunanin ta natsu wajen barin abinda tarihi ba zai manta da shi ba na cigaban kasa.
Ba dole sai kowa ya zama ma'aikacin gwamnati ba, ba dole sai kowa ya zama dan siyasa ba, amma dole ne kowa ya samu hanyar da ba haramtaciyya ba ce na tsayuwa da kafarsa wajen taimakon kan sa da kan sa da sauran jama'a.

Ina jinjinawa gwamnatin nan wajen ganin yadda take kokarin cusa tarbiya da nusar da matasa wajen sanin ciwon kan su, a yau a wannan dakin wasan na hadu da matasa na sassan jihar nan, masu kwazo da sanin ciwon kai wajen kokarin tsayawa da kafarsu dole mu kara masu kwarin guiwa.

No comments