Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gasar Wasan 'Badminton': Ƙuduri Na Zaƙulo Matasa Ya Cika - Muller

Daga Awwal Umar Kontagora An bayyana cewar kudurin dawo da martabar wasan Badmiton da yunkurin zakulo matasa sabbin jini da masu...


Daga Awwal Umar Kontagora

An bayyana cewar kudurin dawo da martabar wasan Badmiton da yunkurin zakulo matasa sabbin jini da masu ruwa da tsaki a harkar suka kuduri aniyar ganin hakan ya cika. Wani jigo a harkar wasan Badmiton, Hon. Ibrahim Abdulhamid ( Muller) ne ya bayyana hakan a cigaba da gasar wasan Badmiton na cin kofin Umar Bago da kungiyar ta shirya a jihar Neja.
Ibrahim Muller, ya cigaba da cewar sama da shekaru talatin ke nan ba a taba yunkuri irin na wannan lokacin ba,  domin tabbas mu Vetran mun nuna da gaske muna son kafa tarihi na janyo matasa masu kwazo dan damawa da su a fagen wasan Badmiton a jihar nan.

Wani abinda na fahimta shi ne nan da yan shekaru jihar nan za ta iya zama daya daga cikin jahohin da kasuwar Badmiton zai daga darajarsu. Kamar yadda manufar shi ne dawo da matasa akan tunani na gari da nuna masu cewar a kowani bangaren akwai rawar da zasu iya takawa, bayan gwarazan da muke alfahari da su a baya yanzu mun fahimci kamar yadda su Aliyu Shehu su ka yi gaba, muna sa ran bada jimawa ba wasu zasu biyo bayan su.

Dan haka zan kara jinjinawa Jawon Minna, Hon. Mohammed Nma Kolo kan irin rawar da yake takawa domin daga cikin yan wasan Badmiton din da muke alfahari da su yau, wasu marayu ne Jawon Minna ke daukar dawainiyar karatunsu da kula da lafiyarsu ka ga wannan abin a yaba ne.
Saboda haka, ina kara jawo hankalin matasa da su zama mutanen da zasu zama abin alfahari, wadanda a gaba kasa za tayi alfahari da su. Dan haka maganar daba da fadace fadacen matasa, ina jawo hankalin matasan mu da su rungumi tsare tsaren gwamnatin jiha na canja tunanin al'umma wajen zama mutanen kirki kuma jagorori na gari.

Hon. Muller, ya ci gaba da cewar da wannan yunkurin na mu muna da yakinin sauran wasanni motsa jiki da aka san jihar nan tayi shuhura akan su bada jimawa ba su dawo domin gwamnati a kowani lokaci musamman gwamnatin Hon. Umar Bago tazo da niyyar dawo da martabar jihar nan, tare da zaburar da matasa muhimmancin tsayuwa da kafarsu, ina jawo hankalin masu ruwa da tsaki a jiha da su zuba jarinsu wajen wasanni motsa jiki ganin duniya a yau wannan bangaren na da muhimmancin sosai ta fuskar samun kudaden shiga da samar da ayyuka ga matasa, bayan kwarin guiwar kiwon lafiya, hanya ce samar da kafar zumunta da taimakekeniya ga matasa da hakan kasa ke cigaba da kawar da zaman kashe wando ga yara masu tasowa.

No comments