Daga Ammar M. Rajab Yawaitar fashi da makami a titin Zariya zuwa Kano ta sanya direbobin manyan motoci masu jigilar kaya kokaw...
Daga Ammar M. Rajab
Yawaitar fashi da makami a titin Zariya zuwa Kano ta sanya direbobin manyan motoci masu jigilar kaya kokawa. Tare da yin kira ga jami'an tsaro da su kawo musu É—auki a hanyar.
Direbobin manyan motocin a Nijeriya sun ce ana yawan samun ayyukan Æ´an fashi da makami inda suke tare titin.
Sun ƙara da cewa; a kwanakin nan da watannin baya kaɗan fashi da makami da daddare ya yaiwata a hanyar a daidai Tashar Tsamiya dake kan titin Zariya zuwa Kano.
Ɗaya daga cikin direbobin manyan motocin dake jigilar kayayyakin masarufi wanda yake yawan bin hanyar mai suna Kamal Muhammad, ya shaidawa jaridar DAILY STRUGGLE cewa; "ko a jiya Talata sun tare hanyar da misalin ƙarfe 1 na dare. Suna haɗa get tare da tara duwatsu a hanya, ɗauke da sanduna da adduna suna yi wa mutane fashi. Da yawansu suna fitowa daga ƙauyukan dake kusa ne, su taru su yi wa mutane fashi", ya labarta.
Ya ci gaba da cewa; "mu dai mun sha da ƙyar, amma sun tare wasu direbobin mu. Ko kwanaki wajen tsere musu sai da suka fasa gilasan mota ta", ya jaddada.
Abubakar Sani, wanda yake direba ne dake yawan kwaso kaya daga Kano zuwa Zariya, ya shaida wa wakilinmu cewa; "lallai tabbas daidai Kwanar Tsamiya kafin ka kai Tashar Yari ƴan fashi da makami na tare hanyar zuwa yi wa direbobi da fasinjoji fashi. Wani lokacin ma ƙarfe 9 na dare suke yi wa mutane fashi", in ji shi.
A ƙarshe direbobin sun yi kira ga jami'an tsaro da su kawo wa hanyar ɗauki tun yanzu kafin lamarin ya wuce gona da iri: "Hanyar Zariya zuwa Kano mahaɗa ce da ta haɗa jihohin Kano, Bauchi, Jigawa Yobe da Borno. Akwai buƙatar hukumomi su kawo wa hanyar ɗauki tun yanzu kafin lamarin ya ƙazance", in ji Abubakar Sani.
Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida mana cewa; "watarana da misalin ƙarfe 9 na dare na dawo daga Kano zuwa Zariya, wani fasinja ya ce zai sauka a daidai Tashar Tsamiya. Direbanmu yana ta faɗa yana cewa da ya san a nan zai sauka, da bai ɗauko shi daga Kano ba. Ai ko direban ya ƙi sauke shi a daidai wurin sai da ya je gaba ya sauke shi. A lokacin direban yake gaya mana cewa fashi da makami ake yi a wurin a kowacce rana da daddare", ya labarto.
No comments