Daga Awwal Umar Kontagora Bayan fara gabatar da wasan Badmiton karo na farko zuwa yanzu yan wasa daga sassan kananan hukumomi as...
Daga Awwal Umar Kontagora
Bayan fara gabatar da wasan Badmiton karo na farko zuwa yanzu yan wasa daga sassan kananan hukumomi ashirin cikin ashirin da biyar suka halarci fara wasar.
Da yake karin haske ga wakilin mu, mataimakin kocin wasar a jihar Neja, Mista Emmanuel Benjemin, yace kamar yadda aka tsara tunda farrko tunda shi ne irinsa na farko akwai bangaren mata wadanda zasu buga Dougble sannan akwai wadanda zasu buga single, haka abin yake a bangaren maza. Bayan nan kowace karamar hukumar ana son ta taho da yan wasa takwas, maza hudu, mata hudu. Amma saboda rashin bada muhimmanci da kuma yanayi wasu kananan hukumomin su zo da mutum daya ne.
Yace daga fara wasan a yau laraba zuwa yanzu mun buga wasa kusan zango goma sha shida, wanda muna kyautata zaton kafin mu kammala wasannin yau zamu kammala wannan zagon sai kuma mu cigaba.
Maganar tarbiya ga yan wasa kuwa, ai mu a bangaren wasanni muna da dokoki komai rashin jin yaro idan ya shigo dole ya natsu. Saboda haka zuwa yanzu ba mu samu kowace irin matsala ba, domin kwamitocin da aka damkawa alhakin shirya wasan sun yi abinda ya dace na tabbatar duk wani abin bukata a wannan wasan sun samar mana da shi.
To, kamar yadda ake zargi ne mu a arewacin kasar nan gaskiya ba a daukar harkar wasan motsa jiki da muhimmanci ba, musamman ma ganin lokuttan da ake samun damar gudanar da wasanni lokutta ne da suka dace da wasu muhimman abubuwan da jama'a suka raja'a akan shi, musamman ma yara a lokuttan ne suke zuwa Islamiyya ko makarantar allo ko dai wani da ake ganin yafi muhimmanci akan wasannin.
Amma duk wanda ka ga ya zama wani abu a duniya a harkar wasanni ya bauta masa ne sosai, wannan yunkurin na kungiyar Badmiton zai taimakawa matasan mu na jihar nan wajen samun shaukin shi musamman daga makarantun sakandare zuwa manyan makarantu.
Ya kamata hukumomin jiha, da su bullo da shirin da zai karfafa yara masu tasowa wajen harkokin wasanni, daga fara wannan wasar na Championship na fahimci idan aka mayar da hankali nan gaba kadan jihar nan za ta yi kafada da kafada da wasu jahohi musamman na kudancin kasar nan a bangaren wasan Badmiton.
Zuwa gobe ne dai ake sa ran cigaba da wasan wanda za a kammala wasan na bana ranar asabar 29 ga watan.
No comments