Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Neja Za Ta Samar Da Keke Napep Mai Aiki Da Wutan Lantarki 5000 Don Samar Da Ayyuka Ga Mata Da Matasa

Daga Awwal Umar Kontagora Gwamnatin Neja ta sha alwashin samar da Keke Napep mai aiki da wutan lantarki dubu biyar da zasu gudan...


Daga Awwal Umar Kontagora

Gwamnatin Neja ta sha alwashin samar da Keke Napep mai aiki da wutan lantarki dubu biyar da zasu gudanar da ayyukan su a yankunan kanannnan hukumomi ashirin da biyar na jihar.

Da take gabatar da jawabinta talatar makon nan a babban dakin taro na tunawa da mai shari'aLegbo Kutigi, kwamishiniyar sufuri a jihar Neja, Hon. Ladidi Idris Kuta, tace wannan shiri ne da gwamnatin manomi Umar Mohammed Bago ya samar dan samun karin gurabun dogaro da kai ga mata da matasa, wanda gwamnati ke yunkurin kawar da rashin aikin yi ga mata da matasa a jiha.

Da yake karin haske ga wakilin Idon Mikiya, daya daga cikin masu ruwa da tsaki a bangaren sufuri, Hon. Danjuma Masu. Yace kamar kwamishinan sufuri ta fada daga cikin kudurin maigirma gwamna shi ne inganta rayuwar matasa da mata tare da taimaka masu wajen dogaro da kafarsu.

Kan haka gwamnati ta sha alwashin samar da wadannan kekunan Napep har dubu biyar a jihar nan.

Yanzu a matakin farko za a samar da guda dubu daya dan fara kaddamar da su a kananan hukumomin Chanchaga, Suleja, Bida da Kontagora, Lapai da Bargu da Bosso wanda mata ne zasu fi cin gajiyar shirin sannan matasa.

Wannan tsarin ba sabo ba ne domin wasu jahohi sun dade da farawa amma a jihar Neja wannan shirin na samar da gurabun sana'o'i ga mata shi ne irinsa na farko, kuma gwamna yayi wannan nazarin ne ganin a kowani yanayi mata sun fi bada gudunmawa wajen cigaban kasa.

Maganar bada keken a matsayin kyauta ba gaskiya ba ne, amma dai gwamnati ta kafa kwamitin da zasu tsara yadda bada Kekunan zai kasance, Kekunan suna da tsaro sosai kuma ana shirye shiryen yadda zasu gudanar da ayyukan su ba tare da tangarda ba, kuma akwai tracker wanda duk inda mutim ya shiga za a gano shi.
Kamar yadda maigirma gwamna ya tabbatar dukkanin kananan hukumomi ashirin da biyar kekunan zasu yi aiki sannan ba maganar neman man fetur ko gas kawai abinda bukata wutan lantarki da za rika caja baturin da keken ke anfani da shi.

Wannan tsarin sufurin zai taimaka wajen samun saukin zurga zurga a wuraren da aka tanadarwa kekunan kuma zai kawo karshen barazanar hauhawar farashin sufuri da ake fakewa da tsadar man fetur ko gas.

Hon. Danjuma Masu, ya shawarci matasa da su rungumi kudurorin gwamnatin jiha hannu biyu domin akwai tsare tsare na inganta rayuwarsu ta hanyar dogaro da kai musamman a bangarorin kasuwanci da noma.

No comments