Daga Awwal Umar Kontagora Kungiyar wasan Badminton ta shirya fara wasan Badminton karo na farko a jihar Neja, wasan mai taken ...
Daga Awwal Umar Kontagora
Kungiyar wasan Badminton ta shirya fara wasan Badminton karo na farko a jihar Neja, wasan mai taken "1st Edition of Farmer Mohammed Umar Bago Inter Local Government Badmiton Championship 2024" zai gudana ne a filin wasa na Minna Polo Club da ke Tunga Minna.
Da yake karin haske ga manema labarai, shugaban kungiyar a jihar Neja, Hon. Mohammed Nma Kolo (Jawon Minna, kuma Amana Agaie) wannan shi ne karon farko da ƙungiyar ta gayyato dukkanin kananan hukumomin jiha su taho su gabza a fagen wasanni, wanda zuwa yanzu kananan hukumomi ashirin sun halarta wanda ake sa ran sauran biyar zasu biyo baya.
Ya ci gaba da cewar bangaren wasanni bangare ne da ke hada kan matasa ta fuskar zaman lafiya tare da karawa matasa damar samun kuzari a cikin shi kuma idan an bi wasu hanyoyin ana iya samun kudaden shiga ga gwamnati.
A cewarsa, gwamnatin Manomi Umar Bago gwamnati ce ke yunkurin samar da hanyoyin zaman lafiya, hadin kai da cigaban kasa, hakan yasa wannan karon battar da za a yi na kwanaki hudu sunan maigirma gwamna.
Muna sa ran kamar yadda manema labarai ku ka ga saukar yan wasan za ku kasance a wannan dandalin dan bada cikakkiyar rahoton abinda ke faruwa ta yadda sauran jahohi za su iya koyi da jihar Neja.
Daga cikin gwarazan da kasar nan ke alfahari da su, jihar Neja muna da gwaraza kamar Aliyu Shehu da ya gwarzon jiha kuma ya taba ciyo kasar kambin Badmiton zai buga wasa a nan, inda zai wakilci kamar hukumar Bida, duk wani fitaccen dan jihar Neja da yayi fice a bangaren Badmiton zai nuna hazakarsa a filin.
Jihar Neja muna tarihi a wannan bangaren kuma muna filaye wadatattu da in har masu hannu da shuni zasu shigo zai kasance an samu damar yin gasa wajen zakulo hazikai da kasar nan za ta rika anfani da su a wasannin duniya ba sai an dauko wasu daga waje ba.
Saboda haka muna kokari ne wajen zakulo hazikan yan wasan da muke da su a boye wadanda suke neman irin wannan damar, da irin wannan ne muka zakulo Aliyu Shehu wanda yau shi ne na biyu a bangaren Badmiton a kasar nan.
Ka muna sa ran zuwan Barr. Frank Obi shugaban Bidmiton na kasa domin mu tabbatar masa da matsayin jihar mu a Badmiton, kuma za mu cigaba da shirya ire-iren wasannin nan domin dawo da tunanin gwamnati kan muhimmancin karfafa wannan sashen, idan Allah ya yarda kowace shekara za mu cigaba da shiryawa.
Irin wadannan wasanni zai baiwa matasa damar nusar da kan su kan kishin kasa, fahimtar juna da kuma samun sana'o'in domin yau duniya ta dauki bangaren wasanni a matsayin wani sashe na samun kudi.
No comments