Daga Awwal Umar Kontagora Hukumar ilimin bai daya ta jihar Neja ta sha alwashin karfafa guiwar malaman makarantun akan bangaren noma. Shugab...
Daga Awwal Umar Kontagora
Hukumar ilimin bai daya ta jihar Neja ta sha alwashin karfafa guiwar malaman makarantun akan bangaren noma. Shugaban hukumar Malam Muhammad Baba Ibrahim Agaie ( Mayakin Agaie) ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta gudanar littinin din makon nan.
Tunda farko a bayaninsa, yace daga cikin kudurin gwamnatin jiha bisa jagorancin Manomi Umar Mohammed Bago na samar da sabuwar jihar Neja, akwai yunkurin canja tunanin al'umma ta hanyar dogaro da kai, musamman dan tsayuwa da kafarsu da kuma samun kudaden shiga ta yadda mutum zai iya tsayuwa da kafarsa.
Hakan yasa hukumar kirkiro wasu hanyoyin da zai taimakawa malamai ta hanyar samar masu da tallafi a bangaren noma wanda hakan zai saukakawa malamai wajen samun saukin gudanar da rayuwarsu na yau da kullun da kuma taimakawa rayuwarsu wajen samun saukin gudanar aikin karantarwa yadda ya dace.
Mayakin Agaie, ya cigaba shirin zai taikamawa malaman da kayan aikin gona da ya kunshi iraruwa, takin zamani da duk wani abinda manomi ke bukata ta hanyar hada guiwa da bangarorin da ke kula da harkar noma musamman hukumar Niger Food da alhakin samar da abinci a jihar Neja ya rataya a wuyanta, a matsayin rance.
Shugaban ya shawarci malaman da ke da niyyar shiga shirin da su guji yin anfani da daliban makarantum su a lokuttan aikin nomar kuma su tabbatar gonakinsu na a yankunan da makarantun suke ba wani bangaren daban ba, dan kaucewa dogaro da kin zuwa wurin aiki a lokuttan da suke kula da gonakinsu.
Muna da makarantu sama da dubu uku bisa kididdgar da aka yi a baya da malamai dubu ashirin da hudu a kasar nan, akwai bukatar samar da kyakkyawar yanayin da za a inganta rayuwar malamai da iyalansu, dole mu hada hannu mu inganta rayuwa ta yadda za a samar da yanayi mai inganci.
Mun sani idan akwai kyakkyawar tsari tabbas za a samu ilimi mai inganci, kuma yanzu gwamnati ta samar da ginshiki mai inganci a bangaren ilimi wanda idan muka bada goyon baya za a anfani shiri yadda ya kamata. Yanzu duniya ta cigaba domin ana samun damarmaki ta hanyar yanar gizo wanda duk ya nema idan ya cancanta zai iya samun wannan damar ba tare da la'akari inda mutum ya fito ba.
Saboda haka inganta rayuwar malamai na da muhimmanci, domin idan aka samu kyakkyawar yaanayi tsarin koyarwa zai inganta kamar gwamnatin jiha ke muradin hakan.
Wannan ne dalilin da yasa muke da kudurin samar da hanyoyin inganta rayuwar malamai, domin ko a karkashin bishiya ake koyarwa idan aka samu tsari mai inganci tsarin koyarwa zai inganta.
Akwai damarmakin da za a inganta rayuwar malamai wannan yasa muke kokarin bullo da wannan tsarin domin bangaren noma yana daga cikin bangaren da ke inganta tattalin arzikin kasa da kuma tsayuwa da kafa, saboda yasa muka zauna da bangarorin da abin ya shafa dan yin tafiyar bai daya ta yadda kowani bangare na kananan hukumomi zasu ci moriyar shirin.
A na sa bayanin, shugaban kungiyar malamai ( NUT) ta jihar Neja, Kwamred Akayabo Adamu Muhammad, yace shiri ne mai kyau. Domin kamar yadda aka sanar da mu yanzu a wannan taron, idan har za a tabbatar da shi ta yadda ya dace, lallai malamai zasu dama ta yadda zasu samu damar rike gidajensu da iyalan su ba tare da dogaro da albashi ba.
Sai kamar yadda shugaban NSUBEB ya fadi ne duk malamin da ya samu wannan damar to ya tabbatar ya kiyaye ya bi tsarin da aka ayyana.
Za mu zauna a matsayin kungiyar NUT mu dubi tsari kuma mu bada shawarwarin da suka dace dan ganin ba samu tangarda ba.
Taron ya samu halartar sakatarori, da shugabannin kungiyar NUT na yankunan kananan hukumomin jihar.
No comments