Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Abba Kabir Ya Canja Salon Siyasarsa Don Mulki Na Hannunsa - Bichi

Daga Awwal Umar Kontagora An yi kira ga gwamnan Kano, Abba Kabiru Yusuf da ya canja salon siyasarsa na tausayi da kau da kai, do...

Daga Awwal Umar Kontagora

An yi kira ga gwamnan Kano, Abba Kabiru Yusuf da ya canja salon siyasarsa na tausayi da kau da kai, domin mulkin Kano ta hannunsa. Wani matash mai fashin baki akan harkokin yau da kullun dan asalin jihar Kano, Malam Shu'aibu Aliyu Bichi ya yi kiran lokacin da yake tsokaci kan matsayin jami'an yan sanda akan rikicin masarautar Kano.

Shu'aibu Bichi, ya ce maganar nadin sarki ko sauke shi yana hannun gwamnatin jiha ne ba gwamnatin tarayya ba, mai makon a ce gwamnatin tarayya ce ke da zabi, da har zai baiwa jami'an tsaro da ke karkashin kulawar gwamnatin jiha daukar bangaranci.

Tausayi, da sanyin zuciyar Abba Kabir ne yasa ake taka shi yadda aka ga dama, wajibi ne gwamnan mu ya tabbatar ya canja wannan yanayin ya tsaya maysayin shi da al'ummar Kano suka amince da ya jagorance su ta hanyar ba shi kuri'a.

"Wannan ba shi ne karon farko ba da ake masa katsalandan a harkokin mulkinsa ba, kuma wannam matakin da yan Abuja ke dauka musamman yan kwangilar APC su sani ba wannan ne zai ba su nasara a zaben gaba ba. Talakawan kasar nan,an yi walkiya sun ga abinda ke boye kuma duk talakan da ke kishin cigaban kasar nan ba zai yarda a sake yaudararsa da kudi ko taliya a lokacin zabuka masu zuwa ba, domin salon mulkin APC kama karya ne ba mulkin dimukuradiyya ba, ita fa dimukuradiyya tsarin mulki ne na jama'a dan jama'a ba bautarwa da kassara jama'a ba.

Saboda haka, ba wani mutum komai girmansa da zai shiga hurumin gwamnatin jiha ba dan kawai yana ganin yana da kusanci da fadar shugaban kasa, ya ga cewar kwarjini ko kima ya ke janyowa gwamnatin ba.

Da ya juya kan kalaman jagoran Kwankwasiyya na kasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, yace dole ce ta sanya shi kalaman masu zafi, wanda an dade ana cin duddugensa, amma hakan ba zai sa hankali ya goshe mu juyawa jagora baya ba, domin yana kishin talakan kasar nan kuma yana son cigaban kasar da jihar Kano.

Ina kira ga matasa kuma magoya bayan gwamnatin jihar Kano da jagora Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, da mu yi hakuri abinda ke gaba yafi baya yawa, tabbas an dade ana taka mu amma cikin hukuncin Ubangiji yau jihar Kano na hannun mu kuma da yardar Allah kuduri da muradun jagora na inganta rayuwar talakan kasar nan zai wanzu bada jimawa ba.

Maganar daukar doka a hannun mu, mu tabbatar mun ajiye shi a gefe, mu zama yan kasa na gari da sauran sassan duniya zasu rika koyi da mu, wajen bada gudunmawa ga zaman lafiya da cigaban kasa.

Matashin ya kara jaddada cewar karya ya kusa karewa dan kada, domin a zabuka masu zuwa talaka ba zai sake yarda ya zabi gaibu ba, domin halin da gwamnatin tarayya ta jefa kasar nan, ya taimakawa talakawa wajen kara wayewa da sanin inda duniya ta sanya a gaba, kuri'un mu ba zasu sake tafiya ga wadanda ba su da kishin kasa ba, tun farko ba su bar shaidar alheri ba, balle ayi tunanin idan sun kan mulki zasu iya tabuka wani abin kirki, yan kan mage ya waye kar talaka ke kallon kowa, ba tsaro, ba zaman lafiya a kasa, masana'antu da kasuwanci kullun kara gurguncewa su ke yi.

A matsayina na matashi, ba mukamin siyasa ko kwangila na ke nema ba, ina muradin samar da shugabanci na dattakoda sanin ya kamata a kasar nan, don haka akidar Kwankwasiyya yanzu muka fara ta, dan burin mu dan talaka ya zama mai alfahari da kan shi, wajen samun walwala da sanin inda rayuwarsa ta sanya gaba.

No comments