Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sarkin Musulmi Ya Ce A Duba Watan Zul-Hijjah A Yau Alhamis

Mai alfarma sarkin Musulmi a Nijeriya, Sa'ad Abubakar III, ya umarci Musulmai su duba jinjirin watan Zul-Hijjah na shekarar Hijira 1445 ...


Mai alfarma sarkin Musulmi a Nijeriya, Sa'ad Abubakar III, ya umarci Musulmai su duba jinjirin watan Zul-Hijjah na shekarar Hijira 1445 a yau Alhamis.

Shugaban kwamitin ba da shawara a kan harkokin addini, Farfesa Sambo Janaidu ya faÉ—a cikin wata sanarwa ya ce "muna sanar da al'ummar Musulmi cewa ranar Alhamis 6 ga watan Yuni za ta zamo daidai da 29 ga watan Zul-Qidah na shekarar 1445 AH".

Sanarwar ta Æ™ara da cewa “ana buÆ™atar Musulmai su fara duba jinjirin watan Dhul-Hijjah, su kuma kai rahoton ganin watan ga dagaci ko hakimin garinsu, domin tura saÆ™on ga mai alfarma sarkin Musulmi.”

Mai alfarma sarkin Musulmin ya yi addu'ar "Allah ya ci gaba da tallafa wa Musulmi wajen gudanar da harkokin ibadar su".

No comments