Tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya ce binciken da majalisar jihar ta ba da shawarar a yi kan gwamnatinsa "bi-ta-da-ƙulli ne kawa...
Tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya ce binciken da majalisar jihar ta ba da shawarar a yi kan gwamnatinsa "bi-ta-da-ƙulli ne kawai na siyasa".
Cikin wata sanarwa da Muyiwa Adekeye ya fitar a madadinsa, El-Rufai ya ce ya bauta wa Kaduna "da gaskiya kuma yana alfahari da abubuwan da ya yi".
A ranar Laraba ne Kakakin Majalisar Dokokin Kaduna Yusuf Liman ya zargi gwamnatin ta El-Rufai da karkatar da kuÉ—in da suka kai naira biliyan 423 da kuma barin jihar da basuka.
Kwamitin da majalisar ta kafa ya ba da shawarar a binciki tsohon gwamnan da kuma wasu muƙarrabansa.
"Muna tabbatar da gaskiyar gwamnatin El-Rufai tare da yin watsi da waɗannan iƙirari da ake yaɗawa," in ji sanarwar.
"Ya bi duk wasu dokoki a ayyukansa lokacin da yake gwamna...ya kamata a yi watsi da wannan binciken na ƙeta a matsayin bi-ta-da-ƙullin siyasa."
No comments