Daga Awwal Umar Kontagora Gwamnan Kebbi Dakta Nasir Idris Ƙauran Gwandu ya naɗa Abdullahi Zuru a matsayin mai bashi shawara akan harkokin hu...
Daga Awwal Umar Kontagora
Gwamnan Kebbi Dakta Nasir Idris Ƙauran Gwandu ya naɗa Abdullahi Zuru a matsayin mai bashi shawara akan harkokin hulda da yan jarida da tsare-tsare.
Sakataren yaɗa labaran gwamnan Alhaji Ahmed Idris ne ya bayyana hakan ranar juma'a 30/8/2024 a lokacin da yake wata ganawa da manema labarai a garin Birnin Kebbi.
Sanarwar ta bayyana cewar sakataren gwamnatin jihar Alhaji Yakubu Bala Tafidan Yawuri ne ya sanyawa takardar shaidar naɗin Abdullahi Zuru a matsayin mai baiwa gwamna shawara akan harkokin hulda da yan jarida da tsare-tsaren yaɗa labarai.
Haka kuma takardar ta bayyana cewar naɗin na Abdullahi Zuru a wannan muƙamin anyi shi ne bisa cancanta da kwarewarsa akan aikin jarida.
Takardar ta bayyana cewar gwamnati na muradin ganin ya nuna ƙwazon da aiki tukuru akan wannan aikin.
Shi dai Abdullahi Zuru tsohon dan jarida ne wanda yake da kwarewa a wannan aikin.
Abdullahi Zuru ya fara aikin jarida ne tun a tsohuwar jihar Sokoto a wani gidan jarida mai suna Concord Group of Newspapers a shekarar 1988 a matsayin mai dauko ma kamfanin jaridar rahotanni daga jihar Sakkwato.
Inda daga nan ya zamo babban bai dauko rahoto daga jihohin Katsina, Kebbi, Borno da kuma Yobe kafin daga baya a naɗa shi matsayin Assistant Bureau-chief in-charge of the Federal Capital Territory (FCT) Abuja.
Haka kuma yayi aiki a matsayin mai tace labarai a kamfanin jaridar Daily trust newspapers kafin kuma daga baya ya koma aiki da kamfanin Thisday Newspapers inda ya zama babban mai tace labarai na yankin Maiduguri.
Haka kuma yayi aiki a matsayin babban mataimaki na musamman akan hulda da kafafen sadarwa da yaɗa labarai na tsohon gwamnan Kebbi Sanata Muhammad Adamu Aleiro, bayan Aleiro ya zama minista ya zama mai bashi shawara akan kafafen yaɗa labarai.
No comments