Daga Awwal Umar Kontagora Gwamnan Kebbi, ya baiwa kungiyar masu saye da sayar da wayoyin hannu shagunan zamani da ta saya akan naira miliyan...
Daga Awwal Umar Kontagora
Gwamnan Kebbi, ya baiwa kungiyar masu saye da sayar da wayoyin hannu shagunan zamani da ta saya akan naira miliyan dari uku. Gwamna Nasiru Kauran Gwandu ne ya bayyana hakan a lokacin mika shagunan hannun su. Ya bayyana cewar gwamnati ta hannuntawa kungiyar shagunan ne domin inganta sana'arsu da kuma bunƙasa harkokin sana'o'in hannu domin dogaro da kai a jihar ta Kebbi.
Da yake jawabi a wurin taron hannunta shagunan ga kungiyar masu sana'ar sayarwa da gyaran wayoyin hannu ta Birnin Kebbi, gwamnan ya bayyana cewar gwamnatinsa a ko da yaushe a shirye take domin ganin ta inganta rayuwar matasa ta hanyar tallafa musu akan sana'o'in dogaro da kai da kuma samar da ayyukan yi ga matasan maza da mata a fadin jihar baki É—aya.
Haka kuma ya bayyana cewar sanin kowa ne gwamnatoci a kowani mataki ba za su iya samar da aikin gwamnati ga kowa da kowa ba, saboda haka gwamnatinsa take bakin ƙoƙarinta wajen ganin matasa sun koyi sana'o'in hannu domin samun aikin yi domin dogaro da kai.
Haka kuma ya bayyana cewar daga cikin wannan ƙoƙarin da gwamnatin jihar take yi, yanzu haka an gina wuraren koyon sana'o'i daban-daban a faɗin jihar baki daya domin samar da aikin yi da inganta rayuwar matasan jihar Kebbi.
Gwamnan ya ƙara da cewar, matashi da ke gudanar da sana'ar hannu zai iya samun kuɗi a sati ko a wata fiye da wanda yake aiki gwamnati.
Dan haka gwamnatin ta saye waÉ—annan shagunan ne waÉ—anda aka fi sani da Olumbo Plaza domin kawo karshen wata takaddama da tsakanin Æ´an kasuwar da mai wurin.
Gwamnan ya bayyana cewar gwamnati ta shigo ciki ne domin ganin an samu mafita ga ƴan kasuwan domin idan gwamnati ba ta shiga ciki ba da yawan ƴan kasuwar harkokin wayar zasu rasa jarinsu saboda haka yasa gwamnatin jihar Kebbi ta saye wurin ta miƙa musu domin cigaba da gudanar da sana'o'insu.
Domin Æ™ara taimakawa Æ´an kasuwan, gwamnan ya umarci sakataren gwamnatin da kwamishinan harkokin kasuwanci na jihar kada a amshi sama da naira dubu hamsin (₦50,000) ga kowani shago a matsayin kudin haya na shekara daya inda gwamnan yace anyi haka ne domin samar da sauÆ™i ga harkokin kasuwanci.
Haka kuma Gwamnan yayi jinjina ga shugabannin kungiyar bisa kokarin da suka yi wajen ganin sun samar da wurin koyar da sana'o'i ga mambobin ta inda yanzu haka wasu har sun kammala kuma an ba su takardar shaida.
A na shi jawabin, shugaban gudanarwar kamfanin Bindawa Enterprises, Alhaji Yahaya Bindawa a madadin mambobin kungiyar, ya nuna jin dadin ƴaƴan kungiyar ga gwamnatin jiha wajen samar musu da shagunan inda yace wannan ba ƙaramin taimakawa ƴan kasuwar zai yi ba.
Daga cikin ababen da suka gudana a wurin taron sun haɗa da kaddamar kasuwar/shagunan sayar da wayoyin wanda aka sauyawa suna zuwa Ƙauran Gwandu GSM Plaza daga sunansa na da wato Olumbo Plaza.
Haka kuma an bayar da da kyautar karramawa ga gwamnan da sakataren gwamnatin jiha da Alhaji Ibrahim Bagudu.
No comments