Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Kaddamar Da Makaranta Da Asibiti Na Mawallafin Jaridar Neptune Prime A Yobe

Daga Idris Umar, Zariya  Mawallafin jaridar Neptune Prime, Dakta Hassan Gimba ya gina makaranta da asibiti a garin Potiskum jihar Yobe. Buki...


Daga Idris Umar, Zariya 

Mawallafin jaridar Neptune Prime, Dakta Hassan Gimba ya gina makaranta da asibiti a garin Potiskum jihar Yobe. Bukin buÉ—e makarantar ya gudana ne a harabar makarantar da ke unguwar Jaji, a ranar Asabar.

Makarantar ta ƙunshi ɓangaren Nursery ne daga aji ɗaya zuwa aji uku. Sai kuma ajin firamare ɗaya (primary one). Iyakacin karatun da za a fara da shi kenan, kafin nan gaba.

A  jawabinsa a wajen taron Dakta Gimba, ya fara ne da godewa Allah (T) da ya kawo mu wannan rana. Ya ce “farin ciki na ba zai misaltu ba. Tun daga jama’ar da na gani a wajen É—aurin aure É—ana, da kuma irin jama’ar da na gani a nan, na rasa ma ta ina zan fara nuna farin ciki na, da kuma godiya jama’a”.

Gimba ya ci gaba da cewa “babu abin da ya fi farin ciki, irin ka ga ka saka mutane a cikin farin ciki. Lokacin rasuwar Mama (Hajiya Hafsat), sai na ga me zan yi da sunanta wadda zai saka mutane a cikin farin ciki, to shi ne na ga gina makaranta da sunanta zai fi.

Da a tunani na, Islamiyya za mu gina, to sai muka tattauna da wani aminina, abokina Abubakar Monja, (Allah ya masa rasuwa) da shi ne muka yi shawarar a gina makaranta É—in. Akwai É—akin na’ura mai Æ™waÆ™walwa (kwamfuta) da muke gina wa, idan aka kammala sunansa za mu saka, Abubakar Monja”.

Sannan an wuce duba Asibitin ‘cutar kansa’ da yake gina wa, domin tuna wa da marigayiya matarsa, wadda aka saka wa asibitin sunanta Hajiya Lami Babare Clinic.

Dakta Gimba ya bayyana gina asibitin domin taimakon al’umma da suke wannan yanki. Sannan al’ummar yankin suna ta murna da farin ciki da samun asibitin. Sun ce yanzu kam nesa ta zo kusa, ganin yadda suke nesa matuÆ™a da babban asibitin garin Potiskum.

Mutane da dama ne suka halarci wajen, sun haÉ—a da wakilin mai martaba sarkin Fika, Alhaji Bukar Abubakar, Shettiman Fika, Hakimi Shayibu (Hakimin Lai Lai), Dakta Mamman Mohammed, Shamakin Fika, Dakta Mamman Mamuda (shugaban kwamitin amintattu na makarantar), Farfesa MK Othman (tsohon Darakta NAERLS, na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, Mista Iliya Joshua (mai magana da yawun hukumar Kwastam ta Æ™asa, reshen Borno da Yobe. Da sauran É—imbim al’umma da suka halarci wannan taro.

Bisa haka da yawa daga cikin editocin jaridu suke fatan alheri ga takwaran nasu bisa wannan namijin kokari da Dakta Hasan Gimba yayi har sun kirashi da suna abin koyi ga al'umma.

An yi taro lafiya an tashi lafiya.

No comments