Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

COYDS Ta Koyar Da Matasa 85 Sana'ar Hannu A Garin Samaru Zariya

Daga A'isha Suleiman Zariya  Yanzu ne daidai lokacin  farfaÉ—o da sana'ar hannu a cikin al'umma don ganin an kori fatara da talau...


Daga A'isha Suleiman Zariya 

Yanzu ne daidai lokacin  farfaÉ—o da sana'ar hannu a cikin al'umma don ganin an kori fatara da talauci a tsakiyar al'umma.

Bisa haka ne cibiyar nan mai suna (Community Organization and Youth Development Services) dake tafi da harkokin ta a makarantar UPE Kallon Kura Hayin Dogo Samaru ta yaye ɗalibai guda 85 da suka hada ɓangarori daban daban da take bada horo a kansu.

Wannan taro ya gudana ne karkashin matashi mai kishi mai kishin matasara wato Comr Shuibu Ishaq Biu Samaru.

Taron ya sami karɓuwa a bangaren iyayen ƙasa da manyan yan siyasar karamar hukumar Sabon Gari da jiha baki ɗaya.

Bayan bude taron da addu'a ne sai shugaban taro Farfesa Ahmad Abdallah Magajin garin Nufe kuma tsohon ministan gona a Nijeriya wanda Farfesa Kabiru ya tsaya a makwafinsa ya bayar da damar ci gaba da taron.

Shi taron an bayyana shi a matsayin karo na farko da cibiyar ta (COYDS) ta fara.

Kuma cikin ikon Allah matasa maza har matan sun nuna kokarinsu sosai wajen tsayawa don koyan sana'ar ta hannu karkashin wannan cibiya.

Da yake bayani Sakataren wannan cibiyar ya ce,suna bayar da horo ne akan bangarori da dama kamar su koyar da ɗinki da koyan ilimin na'ura mai ƙwaƙwalwa (Computer) da koyar da kwalliya da haɗa turaren wuta da turaren wuta yace,kuma duk an sami nasara a dukkan bangarorin.

Bayan Malamai da yan siyasar da sauran jama'a sun gama jawabin goyan baya ga cibiyar. Don neman ci gaba cibiyar ta shelanta neman gudummawa don ci gaban horon da suke bayarwa ga matasan a karon farko.

Manyan baƙi da dama ne suka bayar da tasu gudummawar ciki harda Honorabul Abubakar Jamil Albani ɗan majalisar jihar Kaduna da Honorabul Khalid Soba da Sadik Ango Abdullahi da sauran jama'ar masu yawa maza da mata cikin harda Hajiya Sarauniya Samaru duk sun bayar da tasu gudummawar don ƙarfafa ƙokarin cibiyar.

Bayan kammala taron shugaban cibiyar Comr Shuibu Ishaq ya bayyana jin dadinsa yayin da yake zantawa da manema labarai ya nuna farin cikinsa da jin dadinsa bisa yadda Allah ya nuna mashi wannan rana.

Ya ce, babu abin da zai ce face Allah ya sakawa kowa da Alheri. Kuma ya nemi sauran masu hannu da shuni da su ƙara ba shi goyan baya don ƙara himma akan wannan nasara da aka samu.

Ya yi godiya ga iyayen É—alibai da su kansu É—aliban bisa hadin kan da suka bayar har aka kawo mannan rana.

Ya yi fatan Allah ya mayar da kowa gida lafiya.



No comments