Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tinubu Ya Umarci Matawalle Da Manyan Hafsoshin Tsaron Kasar Su Koma Sakkwato

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bai wa ministan kasa a ma'aikatar tsaro Bello Matawalle da manyan hafsoshin tsaron kasar umarnin ...


Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bai wa ministan kasa a ma'aikatar tsaro Bello Matawalle da manyan hafsoshin tsaron kasar umarnin komawa Sokoto domin tinkarar 'yan bindigar da suka addabi jama'a suna hallakawa ba tare da kakkautawa ba.

Daraktan yada labaran ma'aikatar tsaron Najeriya Henshaw Ogubike ya sanar da wannan umarnin sakamakon karuwar ta'addancin da wadannan 'yan bindiga ke yi a yankin.

Ogubike ya bayyana bacin ran gwamnati dangane da irin ta'addancin da aka gani a yankin arewa maso yammacin kasar, ya yin da yake cewa wannan umarni zai taimaka wajen tinkarar matsalar da kuma tabbatarwa jama'a gwamnati ta damu da halin da suke ciki.

A na shi tsokaci, minista Matawalle ya ce za su jagoranci aikin kawar da Bello Turji da tawagarsa daga yankin.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da wasu daga cikin 'yan ta'addan ke farfaganda da wani faifan bidiyo na kwace wata daga cikin motocin soji tare da konata a Kwashabawa dake karamar hukumar Zurmi.


No comments