Daga A'isha Suleiman Zariya A yanzun haka guguwar siyasa ta fara turnuke jama'ar ƙaramar Hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna. Bisa ...
Daga A'isha Suleiman Zariya
A yanzun haka guguwar siyasa ta fara turnuke jama'ar ƙaramar Hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna.
Bisa haka ne Jaridar Madogara ta garzaya karamar hukumar ta sabon Gari don zakulo ra'ayin jama'a ganin yadda lokacin zaben kananan hukumomi ke ƙaratowa.
Jaridar Madogara ta gudanar da bincike na musamman akan makomar kujerar karamar hukumar Sabon Garin wanda dan majalisar jihar ta Kaduna mai ci a yanzu yake neman hayewa kanta a yanzu haka,wato Honorabul Abubakar Jamil Albani Samaru .
Wanda a gefe guda kuma jam'iyyar adawa ta PDP ta shirya tsaf don dauke wannan kujerar duba da abubuwan da suka faru a lokacin baya .
Bisa haka ne Honorabul Ɗahiru Adamu, Mangal, Samaru ya yi kukan kura ya shelanta cewa wallahi summa tallahi Honorabul Abubakar Jamil Albani shi zai haye kujerar shugabancin karamar hukumar Sabon Gari da ikon Allah ko maƙiya naso ko ba sa so.
Honorabul Mangal ya tabbatar da cewa damar Shiek Albani ya tsaya takaran kujerar shugabancin karamar hukumar Sabon Gari to babu wanda zai nasara a kan shi da ikon Allah bisa abubuwa guda uku.
Mangal ya ce, na farko yanzu siyasa ta canza idan jama'a a bude yake ba maganar rufa-rufa. Duk wanda zai fito takara sai ya nuna mana aikin da ya yi wa jama'arsa. Sheikh Honorabul Abubakar Jamil Albani ba jahilin dan siyasa bane shi don shima idonsa a buɗe yake tar.
Bisa haka ne Honorabul Mangal ya zare takobinsa na yaki tare da shelanta cewa za su yi gidan Albani bisa dacewarsa da ƙoƙarin da yake da shi ga al'ummar da yake wakilta dare da rana.
Mangal ya ce wallahi za su fito kwansu da kwarkwatarsu ranar zabe za su zaɓi Honorabul Abubakar Jamil Albani babu gudu babu ja da baya.
Ƙarshe matashin ya ce a yanzu haka babu wani ɗan siyasa da zai ja da ɗan takarar su a ɓangarori da dama ya ce, shi Honorabul Abubakar Jamil Albani ya fara taimakon jama'a ne tun daga ƙasa har zuwa sama cikin gida da waje ga shi malami ga shi matashi.
Don hakane Honorabul Magal ya yi kira ga daukacin al'ummar Sabon Gari maza da mata da su yi Albani domin shi ne zabin su kuma kuma shi zai kai su ga mafiya a siyasance da ikon Allah.
Ya yi kuma kira ga ya'yan jam'iyyar APC dasu haɗa kansu waje ɗaya don samun nasarar abin da ake nema.
Ya yi fatan Allah ya bai wa jagoran su nasara Honorabul Abubakar Jamil Albani Samaru .
No comments