Daga Awwal Umar Kontagora An bayyana cewar ya kamata majalisar dokokin jihar Neja da gwamnatin jiha da su farka daga mafakar da suka baiwa w...
Daga Awwal Umar Kontagora
An bayyana cewar ya kamata majalisar dokokin jihar Neja da gwamnatin jiha da su farka daga mafakar da suka baiwa wasu kungiyoyin da suka fake da rigar tsaro suna yiwa gwamnati zagon kasa akan nasarorin da ta fara samu kan matsalar tsaro a jihar. Shugaban matasan kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders ta kasa kuma kodinetan kungiyar Bago Ruga-Ruga, Comr. Abubakar Babangida yayi kiran a lokacin da yake martani kan rikicin Barkuta da ke gundumar Beji na karamar hukumar Bosso.
Comr. Babangida ya cigaba da cewar, rikicin Barkuta ba rikicin manoma da fulani ba ne, rikici ne na fulani da yan banga, domin an zargi wani da laifi ya kamata a tabbatar an kamo mai laifin nan an mika shi hannun hukumomin tsaron da aikin ya rataya a wuyan su ne, domin ba dokar da ta baiwa yan banga hurumin kamawa da tsarewa, amma sun koma bin rugagen fulani suna kone gidajen al'umma, ba su tsaya nan ba, sun koma kan hanyoyi suna kama mutane suna kashewa, domin ya faru da dan uwan mu akan hanyarsa ta zuwa Rijau daga minna, yan banga ne suka kashe shi.
Saboda haka abinda muka sani a baya, idan an samu rashin fahimta tsakanin manoma da makiyaya masu ruwa da tsaki na yankin su ke shiga su sulhunta.
Yau idan an ce an kafa banga saboda maganar barayi ne, wani dan banga ne bai san inda barayin nan suke ba, can ya kamata su tafi su nuna kwazon su, ba su dawo cikin gari suna farwa jama'a ba, ya zama wajibi idan gwamnati da gaske ta ke duk masu ruwa da tsaki da su hada guiwa wajen nazarin abubuwan da yan bangar nan ke yi, domin daidaita ayyukan su, amma kusan wadannan kungiyar jinsin yare daya ke jagorantarsu, ta ina idan abu ya faru zasu tsaya su yi aiki bisa adalci.
Maigirma Kwamishinan ma'aikatar jin dadin manoma da makiyaya a kullun yana kira ga matasa da su zama jakadun zaman lafiya, shi yasa a kowa ne lokaci matasan fulani ke mutunta doka, amma muna jin tsoron abubuwan da aka gagari shawo kan su a jahohin Zamfara, Katsina da Sokoto ya zama silar cigaba da faruwa, domin irin wadannan matsalolin da yan banga ke haddasawa ne ya janyo shi.
Shugaban matasan na kasa, yace kasar nan akwai sojoji da yan sanda kuma akwai jami'an tsaro na farin kaya, bai kamata su bar aikinsu na lalacewa akan wadanda ba su da kwarewa akan sha'anin aikin tsaro ba, ya kamata tunda kasar nan akwai doka to koma waye a tabbatar an hukunta shi bisa dokar kasa, ba hukunci na rashin adalci ba.
Ina kara jaddawa gwamnatin jiha da majalisar dokokin jiha da su tabbatar sun tadiye masu yiwa gwamnatin jiha zagon kasa akan nasarorin da aka fara samu zuwa yanzu, domin kar sanya idanu ya sake gurgunta inda aka sanya a gaba.
Comr. Babangida, ya nemi matasan fulani da su kai zucîyarsu nesa, su baiwa junansu hakuri kan abubuwan da ke faruwa, domin manya sun tsaya zasu tabbatar gwamnati da jami'an tsaro sun yi abinda ya dace.
Rikicin dai ya lakume rayukan mutane shida bayan rugagen fulani da ake zargin yan banga sun cin na ma wuta, wadanda fulanin da aka yiwa ta'adin suna zaune a yankin ne shekaru da dama, suna noma suna kiwo a matsugunnin na su.
No comments