Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mauludi: Gwamnan Kebbi ya baiwa ƙungiyar Ɗariƙar Tijjaniyya tallafin Naira miliyan hamsin

Daga Awwal Umar Kontagora Gwamnan Kebbi Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu ya baiwa kungiyar Ɗariƙar Tijjaniyya tallafin Naira miliyan...


Daga Awwal Umar Kontagora

Gwamnan Kebbi Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu ya baiwa kungiyar Ɗariƙar Tijjaniyya tallafin Naira miliyan hamsin (₦50m) domin cigaba da hadimar addinin musulunci.

Gwamnan ya bayar da tallafin kuɗin ne a wurin taron Mauludin Sheikh Ahmadu Tijjani na wannan shekarar 2024 da ya gudanar  Lahadin nan 1/9/2024 a babban filin wasa na Haliru Abdu da ke Birnin Kebbi.

Ƙungiyar Ɗariƙar Tijjaniyya ta ƙasa ce ta shirya taron kuma ta zaɓi jihar Kebbi a matsayin jihar da za'a gudanar da taron na bana.

Da yake jawabi a wurin taron, Gwamna Nasir Idris Ƙauran Gwandu ya bayyana cewar a shirye gwamnatinsa take wajen taimakawa dukkanin wata kungiyar addini da za ta taimaka wajen yaɗa addinin musulunci inda yayi kira ga kungiyar ta dariƙar Tijjaniyya da su kara ƙaimi wajen yaɗa addinin musulunci.

Haka kuma gwamnan yayi godiya ta musamman ga kungiyar bisa irin goyon bayan da suka ba shi a lokacin yaƙin neman zaɓe inda kuma yayi amfani da wannan damar yayi maraba da baƙin da suka zo taron daga ƙasashen Morocco, Senegal da Algeriya.

Sheikh Ibrahim Ɗahiru Usman Bauchi da yake nasa jawabin tun a farko a wurin taron, ya bayyana cewar babban maƙasudin taron shine tunawa da irin gudunmawar da Sheikh Ahmadu Tijjani ya bayar ga cigaban addinin musulunci a faɗin duniya.

Haka kuma ya bayyana cewar kungiyar za tayi amfani da wannan taron wajen gudanar da addu'oin neman zaman lafiya a Najeriya dama duniya baki ɗaya.

Haka kuma yayi godiya ta musamman ga gwamna Kebbi, bisa irin gudunmawar da yake baiwa kungiyar duk lokacin da hidimarta ya taso. 

No comments