Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ambaliyar Ruwa: Babban Daraktan N-HYPPADEC Ya Shirya Taron Manema Labarai

Daga Awwal Umar Kontagora Ambaliyar ruwa na É—aya daga cikin annobar da ke faruwa a Nijeriya, rahoton hukumar bada agajin gaggawa...


Daga Awwal Umar Kontagora

Ambaliyar ruwa na ɗaya daga cikin annobar da ke faruwa a Nijeriya, rahoton hukumar bada agajin gaggawa ta Kasa (NEMA) na shekarar 2024 ya nuna cewar, ambaliyar ruwa ta raba sama da mutane 208,000 da muhallansu tare da laƙume rayuka kusan 200 a jihohi 28 daga cikin 36 na ƙasar nan.

Babban daraktan hukumar tallafawa al'umomin da ke zaune a yankunan da ke samar da wutar lantarki ta Ƙasa (N-HYPPADEC) Abubakar Sadiq Yelwa FCNA, FNIM (Katukan Yauri)  ya bayyana hakan a wani taron manema labarai inda ya bayyana cewar jihohin N-HYPADEC ke kula da suna fuskantar ambaliyar ruwa a duk shekara sakamakon ayyukan samar da wutar lantarki da ruwa  a waÉ—annan wurare.

 Babban daraktan ya Æ™ara da cewar kusan kashi 80% na al'ummar Æ™asar nan da suka fi fama da annobar suna cikin jihohin N-HYPPADEC da kadarorin miliyoyin Nlnaira da gonakin noma.  "Ƙaramar barazanar sauyin yanayi da ta Æ™ara dagula haÉ—arin da al'ummomin yankunan ke fuskanta ya sa aka yi kira ga wannan taron manema labarai da ya jawo hankalin masu ruwa da tsaki a kan matakan gaggawa na magance matsalar". 

Babban daraktan ya bayyana cewar kimanin al’ummomi É—ari shida da talatin da huÉ—u (634) ne suka salwanta da gonaki kusan dubu talatin (30) da aka rasa a jihar Binuwai, haka ma a jihar Kebbi inda gidaje dubu shida da É—ari tara da hamsin da tara (6,959) suka shafe tare da kwashe gonaki kusan dubu goma (10,000), haka kuma a jihar Gombe irin É“arnar da aka samu ba kaÉ—an ba ne.  Ambaliyar ruwa na bana na daga tashar wutar lantarki ta DaÉ—in kowa ba kawai ta yi barazana ga dukiyoyi ba har ma da rayukan al'ummomin da abin ya shafa.

Ya yi nuni da cewar, cigaban hakan na zama wani babban cikas ga yunÆ™urin gwamnatin Nijeriya na samar da abinci da kuma yunÆ™urin shugaba Bola Ahmed Tinubu na samar da ingantacciyar Nijeriya ta hanyar samar da arziki don hanzarta bunÆ™asa tattalin arziki da cigaban kasa. 

Domin daÆ™ile illar É“arnar ambaliyar ruwa ga al’ummar da hukumar N-HYPPADEC kulawa da su, Babban daraktan ya bayyana cewa hukumar ta gina sama da gidaje É—ari biyar a faÉ—in jihohin N-HYPPADEC shida da suka haÉ—a da jihohin Benue, Kebbi, Kogi, Kwara, Niger da Plateau ga waÉ—anda ambaliyar ruwa ta shafa. Ya ce baya ga ayyukan ambaliyar ruwa da zaizayar Æ™asa a jahohin Kogi, Kwara, Binuwai da Kebbi da kuma wayar da kan kafafen yaÉ—a labarai muhimmancin wayar da kan jama'a, illar ziyarar kasa, da bada shawarwari kan illolin ambaliya da sauran batutuwan da suka shafi hakan. 

 Shugaban na N-HYPPADEC na kasa, da yake bayyana damuwarsa kan cigaban annobar da jin daÉ—in yadda al’ummar da abin ya shafa suka sadaukar da gidajen kakanninsu da gonakinsu domin shimfiÉ—a hanyoyi da ayyukan gina madatsun ruwa na samar da wutar lantarki a Æ™asar nan, Sadiq Yelwa, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ayyana tallafi na gaggawa a jihohin N-HYPPADEC. 

Abubakar Yelwa ya kuma yi kira da a haÉ—a kai a tsakanin masu ruwa da tsaki, masu hannu da shuni da ‘yan Nijeriya masu kishin Æ™asa da su kai É—auki ga waÉ—anda abin ya shafa.

Ya kuma yaba wa mai girma shugaban Æ™asa Bola Ahmed Tinubu GCFR bisa matakin gaggawar da ya É—auka na bayar da umarnin sakin kuÉ—aÉ—en tallafi ga jahohin da ambaliyar ruwa ta shafa sannan ya buÆ™aci al’ummar da ke zaune a filayen da ambaliyar ruwa ta shafa a faÉ—in Æ™asar nan da su yi taka-tsan-tsan tare da bin umarni daga  hukumomin da suka dace a kan Æ™a'idojin kariya.

No comments