Daga Awwal Umar Kontagora Ƙaramar hukumar Chanchaga ta tallafawa mata masu kananan sana'o'in da jari su dubu daya da dar...
Daga Awwal Umar Kontagora
Ƙaramar hukumar Chanchaga ta tallafawa mata masu kananan sana'o'in da jari su dubu daya da dari daya a gundumomin mazabu goma sha daya na karamar hukumar.
Tunda farko da yake bayani lokacin kaddamar da shirin bada tallafin, shugaban karamar hukumar, Hon. Aminu Yakubu Ladan, ya ce sun ɓullo da wannan shirin ne dan tallafawa mata masu kananan sana',o'in hannu saboda yunkurin gwamnatin jiha na karfafa guiwar wadanda suka dogara da karfarsu ta hanyar sana'a.
Kowanne gundumar mazaba mun zakulo mata dari da muke yunkurin tallafa masu da jarin naira dubu goma goma, yayin da wasu zasu samu tallafin naira dubu ashirin, wadanda su ka zo a karkashin kungiya kuma zasu samu tallafin naira dubu hamsin.
A cewar shugaban karamar hukumar mun ware naira miliyan ashirin dan cin ma wannan kudurin. Bayan nan majalisar karamar hukuma za tayi nazari kan kudaden shigar da yan kasuwa ke samarwa karamar hukuma, babban kudurin mu a nan, duk wanda jarin da yake juyawa bai wuce naira dubu dari biyar ba karamar hukuma za ta janye karban haraji a hannun sa.
Hon. Aminu Ladan, ya roki iyaye da su kara kaimi wajen kulawa da tarbiyar yayan su, domin karamar hukuma.ba za ta juri fadar daba a minna ba, mun ja layi kuma duk wanda yace bai yarda ba, idan ya fito za mu fito, idan ya riko adda ko gariyo za mu dauko bindiga duk wanda ya kashe tabbas za mu kashe shi, domin hakkin gwamnati ne kare rayuka da dukiyoyin jama'a.
Shugaban, ya ce mun bullo da shirin horar da matasa ilimin sarrafa na'ura mai kwakwalwa (Computer) kudurin mu shi kafin karshen shekarar 2024 din nan da muke ciki za mu horar da matasa a karamar hukumar nan dubu biyar dan rage zaman kashe wando da samar da ayyuka ga matasa.
Wannan tallafin ba ajalan ba ne, duk wanda Allah ya ciyar mun ba shi fom dan tabbatar da cewar shi aka zabo zamu karbi fom din nan take mu ba shi abinda Allah ya ciyar da shi nan take.
Wadanda muka fara tabawa a yanzu sune wadanda jarin dubu goma zuwa ashirin zai iya tasiri a cikin sana'o'in su, ta yadda za mu karfafa masu guiwa, kuma wani ya zagayo ta baya yace yazo karban kwamisho, ba ya da wannan hakkin kar su yarda su baiwa kowa komai ko kuma a ce su raba da wasu, hakkin su ne da Allah ya ciyar da su.
Shugaban, ya nemi masu hannu da shuni da su rika taimakawa al'umma da arzikin da Allah ya ba su musamman a irin wannan lokacin da al'umma ke cikin mawuyacin hali, gwamnati na kokarin ta amma dambu ne idan yayi yawa baya jin mai.
Haka kuma, yayi kira ga al'ummar jihar Neja da su cigaba da baiwa gwamnatin jiha da kananan hukumomi goyon baya, akwai kudurce kudurce masu alfanu da maigirma gwamna babban Manomi ya kudurta dan cigaban tattalin arzikin al'umma da jihar Neja baki daya.
Taron dai ya samu halartar mataimakin shugaban karamar hukumar ta Chanchaga, Malam Isah Muhammad, da majalisar kansulolin karamar hukumar, da shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar, Hon. Albashir, masu unguwanni bisa jagorancin gundumar Makera da wasu gaggan yan siyasa, inda shugaban karamar hukumar ya bada tabbacin zai kammala rabon tallafin cikin kwanaki hudu a dukkanin gundumomin zabe goma sha daya na karamar hukumar.
No comments