Daga Idris Umar, Zariya A cikin wannan satin da ya gabata ne ɗaya daga cikin fitattun ƴan siyasar ƙaramar hukumar Sabon Gari jih...
Daga Idris Umar, Zariya
A cikin wannan satin da ya gabata ne ɗaya daga cikin fitattun ƴan siyasar ƙaramar hukumar Sabon Gari jihar Kaduna wato Honorabul Yunusa Boy ya shaidawa duniya cewa Sanata su na fita kunya ne.
Ya yi wannan furucin ne a yayin da yake zantawa da manema labarai a wajen wani taron harkar Ilmi da ya gudana a garin Samaru.
Yunusa Boy ya ce har yanzu ba a sami wani Sanata ba mai faɗa a cika kamar Sanata Ibrahima Khalid Soba.
Ya ce a yanzu haka babu inda Sanatan bai taɓo ba bakin gwargwadon iko.
Ya ce ya ji wasu na surutai akansa akan hakan ne yake ba su haƙuri da cewa su kwantar da hankulan su Sanata bai manta da su ba.
Honorabul Yunusa ya ƙara da cewa a wannan lokacin ya waiwayi ɗalibai ne domin an ce ilimi shi ne ƙashin bayan rayuwa to yanzun haka ya bai wa ɗalibai tallafin ci gaba da karatu adadi masu yawa
Tuni Honorabul Yunusa ya sake tabbatarwa da al'umma cewa yanzu haka Sanatan zai waiwayi mata don suma su shaida romon dimokuraɗiyya.
Ƙarshe ya yi roƙo da cewa duk wani ɗan siyasa da wanda ba ɗan siyasa ba da ɗan PDP da wanda ba ɗan PDP ba duk Sanata na shirin yin alherin da kowa zai dara a lokaci kaɗan mai zuwa.
Bisa haka ya nemi jama'a su ƙara taimaka masa da addu'a ta goyon baya.
No comments