Daga Awwal Umar Kontagora Hukumar kidaya ta kasa reshen jihar Neja zasu horar da yan yiwa kasa hidima dan aikin kidayar yara kanana masu kar...
Daga Awwal Umar Kontagora
Hukumar kidaya ta kasa reshen jihar Neja zasu horar da yan yiwa kasa hidima dan aikin kidayar yara kanana masu karancin shekaru da ake shirin farawa.
Da yake jawabi a taron bude shirin horarwar, Hon. Muhammad Dattijo Usman ( Ubandoman Minna) kuma shugaban kwamishinan hukummar a jihar Neja. Yace akwai tasgaro wajen samun rajistan yayan da ake haihuwa wajen tattara bayanai da samun cika kudin jimlar al'ummar kasar nan.
Dattijo, yace abinda ake bukata shi ne a lokacin aikin a samu cikakken bayanin jaririn da aka haifa ta yadda zai samu shiga cikin kundin yawan al'ummar kasa, tare da tabbatar da cewar jaririn ya samu NIN ta yadda ko ya girma ba za a samu matsala ko wahala wajen samun sanya shi cikin kundin jimlar yan kasa ba.
Kwamishinan yace ba wai dole sai jaririn da aka haifa yau ko jiya, duk karamin yaron da iyayensa suka tabbatar bai da takardar haihuwa, ana iya yiwa masa wannan rajistan, hakan zai taimakawa gwamnati wajen shirya kasafin kudinta wajen ayyukan raya kasa.
Horarwar ko bitar da hukmar da hadin guiwar Unicef suka shirya zai kwashe kwanaki uku, wanda za a horar da mutum dubu daya da dari shida da tamanin, wanda zasu gudanar da ayyukan su a kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar Neja.
Ubandoman Minna, yace aiki da za a gudanar da shi cikin makwanni uku wanda hukumar za ta tabbatar an shiga lungu da sakon jihar nan ganin an samu nasarar aikin kamar yadda ake fata.
Kwamishinan yace fatan mu shi ne samun rajintan mutum dubu dari biyu da saba'in da shida a jihar nan. Manufar shirin akwai kudurorin gwamnati akan al'umma ta fuskar ilimi da kiwon lafiya, wanda idan ba a da jimlar yawan al'umma sai ayi ta noma akan fako domin ba a san inda kudurin da ake kokarin cin mawa ya dosa ba.
Anfanin wannan rajistan, shi ne kasa ta san da zaman ka, wanda duk wani kuduri na kiwon lafiya, ilimi da ayyukan raya kasa kai ka mora, saboda haka muna jawo hankalin iyayen yara da su marawa shirin baya na tabbatar da cewar yayan su sun samu cikakken rajista a matsayin su na yan kasa. Ta yadda idan gwamnati ta zo tsare tsaren kasafin kudi kaima za ka samu shiga ciki.
Nma Alhaji Shehu, darakta hukumar yace manufar janyo masu ruwa da tsaki musamman sarakuna da iyayen al'umma, shi ne ta yadda zasu tabbatar sun samu cikakken bayani ta yadda zasu wayar da kan al'uumomin da suke jagoranta muhimmancin wannan aikin.
Saboda haka, muna jawo hankalin masu ruwa da tsaki da su zama wakilai na gari kuma iyayen da zasu taimakawa al'uumomin su duk wani abu na cigaban kasa. Wadanda zasu gudanar da ayyukan nan kamar yadda kwamishinan hukumar mu ya fada, na daga cikin wadanda suna nuna kudurinsu na taimakawa dan ganin aikin ya samu nasara, wanda a karshe idan an kammala akwai dan hasafin da za a ba su sakamakon gudunmawar da suka bayar.
Hon. Isah Mohammed, shi ne mataimakin shugaban karamar hukumar Chanchaga, yace mu tuni muka karbi shirin hannu biyu, yanzu haka karamar hukuma ta samar da matsugunni ga jami'an da zasu gudanar da wannan muhimmin aikin a cikin sakatariyar da ke cikin garin minna.
Dan haka ina jawo hankalin iyayen yara da su tabbatar duk wanda bai samu damar yiwa yaron shi rajista a lokacin haihuwarsa ba, to ga dama ta samu iyaye su tabbatar an yiwa yayan su rajista.
Mataimakin na shugaban karamar hukumar Chanchaga, yace karamar hukuma za ta tabbatar duk masu ruwa da tsaki a karamar hukumar nan sun wayar da kan al'uumomi muhimmancin wannan kidaya dan tabbatar da cewar karamar hukumar Chanchaga mun sakamako mai kyau.
No comments