Daga Hussaini Yero Uwargidan Shugaban Kasa, Sen. Oluremi Tinubu ta jinjina wa kananan ‘yan kasuwa mata bisa jajircewarsu da dorewar harko...
Daga Hussaini Yero
Uwargidan Shugaban Kasa, Sen. Oluremi Tinubu ta jinjina wa kananan ‘yan kasuwa mata bisa jajircewarsu da dorewar harkokin kasuwanci su duk da kalubalen da ya shafi tattalin arziki, kuma a nan take ta ba matan dubu daya tallafin jarin dubu hamsin domin bunkasa kasuwancin su a Zamfara.
Uwargidan Shugaban kasar ta bada tallafin ne ga kananan 'yan kasuwa mata 1000 jari a Zamfara ta hannun Uwargidan gwamnan Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal.
Oluremi Tinubu ta bayyana cewa, kananan ‘yan kasuwa mata 1000 da suka ci gajiyar shirin, a Zamfara, domin bunkasa kasuwancin da tattalin arzikin jihar ta Zamfara.
“Dukkan mu muna sane da kalubalen da kanana da matsakaitan masana’antu ke fuskanta musamman ‘yan kasuwa masu karamin karfi, wadanda su ne kashin bayan tattalin arzikinmu na cikin gida.
“Muna murnar kwazon ku da jajircewarku, mu ci gaba da hada kai don gina Nijeriya da kowace mace za ta samu damar yin karamar sana’a da za ta bunkasa da kuma ba da gudummawa ga ci gaban kasarmu.
"Baiwa mata ’yan kasuwa 1,000 da aka zaba a jihar tallafin Naira 50,000 kowannensu don dawo da jari da bunkasa kasuwancinsu.
"Tallafin kasuwanci da aka bayar shi ne don taimakawa mata kanana ‘yan kasuwa wajen shawo kan wasu matsalolin kasuwanci, fadada kasuwancinsu, samar da karin ayyukan yi, da inganta tattalin arzikin kasa.
A nasa jawabin Kwamishinan kasuwanci da yawon bude ido, Alhaji Abdulrahaman Tunbido ya yabawa gwamnatin tarayya bisa wannan gagarimin shirin kuma ya zo akan lokacin da ake bukatarsa.
Tunbido ya ce jihar Zamfara ta riga ta fuskanci matsalar rashin tsaro ta yadda ta ruguje duk wani bangare na rayuwa, dole ne mu yaba da wannan matakin domin zai taimaka wajen ganin an ceto mutanen mu".
"Wannan shirin ya yi daidai da kudirin Gwamnan Dauda Lawal na bunkasa kananan 'yan kasuwa da kasuwanci.
No comments