Daga Awwal Umar Kontagora An yi kira ga kwamishinan ma'aikatar jin dadin manoma da makiyaya, Hon. Umar Sanda Rabe da ya dauki kwararan m...
Daga Awwal Umar Kontagora
An yi kira ga kwamishinan ma'aikatar jin dadin manoma da makiyaya, Hon. Umar Sanda Rabe da ya dauki kwararan matakai na samun sulhu a tsakanin su, domin manomi da makiyayi ba wanda ya isa ya shiga tsakanin su. Al'ummomi ne da tarihi ya tabbatar da zumunci a tsakanin su, saboda haka maganar samun sabani a tsakani wajibi ne, amma a daina barin tunani na yin nisa da hankali. Wani mai fashin baki akan harkokin yau da kullun kuma tsohon manomi, Alhaji Hanza Yanga Buba yayi kiran asabar din makon nan lokacin da yake tsokaci kan rikicin da ya taso a kauyen Barkuta da ke gundumar Beji na karamar hukumar Bosso da ya kai ga cin rayuka da dama.
Dattijon, ya cigaba da cewar tunda muka taso mun ga irin wannan na faruwa, amma ba a yin rashin hankali irin wannan tunda sarakunan gargajiya na al'umma da sarakunan fulani ke zama suna walwale duk wata matsala ko rashin fahimtar juna idan ta taso tsakani manomi da makiyayi, ya kamata wannan ma'aikatar ta farfado da irin wannan tsarin dan kaucewa barin al'umma na daukar doka a hannun su.
Ya kamata jami'an tsaro su tsaya matsayinsu na kare rayuka da dukiyoyin jama'a, idan aka bari abubuwa na rincabewa irin haka, ba a kama hanyar zaman lafiya ba, domin maciji ne aka dukunkune kan shi a tsumma alhalin yana raye, wanda idan ya tsira ba a san irin barnar da zai yi a gaba ba.
Ya kamata, wannan ma'aikatar ta bullo da tsarin tattara bayanan dukkanin makiyayan jihar nan, a san matsugunnan su, sannan a san wuraren da suke zuwa rani da lokacin dawowarsu, hakan zai bada damar tantance na gari da mugu kuma zai taimaka gaya wajen samun cikakken tsaro dan kaucewa fadawa tarkon masu haddasa fitina a cikin al'umma.
Dattijon, yace maigirma gwamna Umaru Bago yayi tunani mai zurfi na kirkirar wannan ma'aikatar, ya kamata ta jajirce wajen cin ma kudurin gwamnatin jiha na samar da turbar zaman lafiya tsakani makiyaya da manoma, hakan zai taimaka wajen farfado da harkar noma da kiwo a jihar nan, amma abubuwan da ke faruwa a yanzu ba su da dadin ji domin hankali da tunani ba zasu lamunci wannan ba.
Idan makiyaya ko manoma na aukawa junan su, wani cigaba wannan gabar zai kawo, ba cigaba illa koma baya da mayar da tattalin arziki baya, saboda haka akwai bukatar dukkanin bangari su kai zuciyarsu nesa su yi aiki da hankali, a kowace gunduma ko matsugunni akwai shugabanni, ya kamata duk abinda ya taso a sanar da su, idan sun kasa daukar matakai ne za a tuntubi hukumomin da abin ya shafa ba daukar mataki ko ramuwar gayya ba.
Ina kara kira da babban murya ga sarakunan gargajiya na jihar nan baki daya, da su rungumi zaman lafiya, su rika umurtar wakilan su da ke tare da talakawa da su rika shirya taruka na masu ruwa da tsaki a yankunan da suke jagoranta dan tattauna matsalolin da ke tasowa a yankunan su suna sanar da iyayen kasa da kuma daukar shawarwarin bai daya ta yadda za a samu zaman lafiya a tsakanin al'ummomin da suke zaune da juna.
Dattijon, ya roki dukkanin bangarorin da matsalar rikicin Barkuta ya shafa da su yi hakuri su kai zuciya nesa dan ba wanda ya isa ya kori wani ko ya tada wani domin ba yadda za a cigaba muddin babu fahimtar juna.
No comments