Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ayyukan Raya Kasa: Majalisar Kansilolin Chanchaga Sun Sha Alwashin Cigaba Da Karfafa Shugaban Karamar Hukumar

Daga Awwal Umar Kontagora Majalisar kansulolin karamar hukumar Chanchaga ta jihar Neja, ta sha alwashin cigaba da karfafa guiwar shugaban ka...


Daga Awwal Umar Kontagora

Majalisar kansulolin karamar hukumar Chanchaga ta jihar Neja, ta sha alwashin cigaba da karfafa guiwar shugaban karamar hukumar, Hon. Aminu Yakubu Ladan dan cigaba da ayyukan raya kasa da taimakon jama'a. Shugaban masu rinjaye na majalisar kansulolin, Hon. Ibrahim Isah Gomna kansula mai wakiltar gundumar Minna ta kudu ya bada tabbacin a lokacin rufe gangamin tallafawa mata masu karamin karfi da shugaban karamar hukumar ya fara a zangon farko.

Hon. Ibrahim Gomna, yace a yanzu shugaban karamar hukuma ya kashe naira miliyan ashirin akan wannan muhimmin aikin, za mu koma a matakin majalisa idan mun ga abinda ya shigo aljihun karamar hukuma yana da rata, za mu karfafa guiwarsa zuwa miliyan talatin zuwa hamsin.

Gwamnati ba ta iya baiwa kowa aiki, amma da tana da damar karfafa guiwar masu karamin jari ta yadda zasu fadada sana'o'in su, wannan kudurin na karfafa guiwar mata dubu daya da dari daya a gundumomin mazabu sha daya a kamarar hukumar nan abin a yaba ne.

Da yake tsokaci, wani matashi a karamar hukumar, Muhammad Abdullahi ( Amb. Mujaheed) yace wannan kalubale ne gare mu matasa, in har shugaban karamar hukuma da bai wuce shekaru talatin da biyar da haihuwa ba, zai yi irin wannan tunanin na taimakawa iyayen mu mata, to ban ga dalilin da zai sa matasa su shiga aikin daba, sara suka da bai mayar da su komai sai koma baya.

Ya kamata, matasa mu natsu mu fara tunanin wani matakin Hon. Aminu Ladan ya bi ya cin ma wannan matsayin da har yau yana tunanin taimakawa iyayen mu, da mu ma zamu gwada basira da tunanin mu wajen kawo cigaba ga al'ummar mu.

Wannan shi ne irinsa na farko a karamar hukumar Chanchaga da shugaban karamar hukuma zai fito ya zagaye al'ummar da suka zabe shi kuma ba zagaye haka siddan ba, zagaye ne mai ma'ana na tallafawa iyayen mu mata masu kananan sana'o'i, wannan karon farko ne fa, idan kananan hukumomi suka samu kudaden su kai tsaye Allah ne kadai yasan romon mulkin dimukuradiyyar da za mu sha karkashin mulkin wannan bawan Allah.

A bayaninsa bayan rufe bada tallafin a gundumar mazabar Minna ta kudu, bayan guudumomin Tudun-Wada ta arewa da kudu da ya gabatar a lahadin makon nan, shugaban karamar hukumar yace ya fara da iyaye mata da matasan mata masu kananan sana'o'i ne domin suna bukatar kulawar gaggawa kuma akwai shiri na gaba nan bada jimawa ba, wanda za a bada wani kason ga wadansu sashen yan kasuwa, yace dukkan wannan kuduri ne na gwamnatin tarayya da ta jiha karkashin mulkin babban manomin jiha, Hon. Umar Mohammed Bago ta yadda za a karfafa guiwar masu kananan sana'o'i ta yadda za su tsaya da kafarsu.

Hon. Aminu Ladan, yace wannan tallafin ya bada shi ne ta yadda masu kananan sana'o'i zasu fahimci cewar gwamnati ta damu da halin da suke ciki, kan haka aka bullo da bada tallafin a matsayin kyauta ba wai bashi ne da za su biya ba.

Dan haka, ya hori dukkan wadanda suka ci gajiyar tallafin da su yi anfani da kudaden wajen bunkasa sana'o'in su, ta yadda suma zasu iya tsayuwa da kafarsu wajen habbaka sana'o'in su.

Taron dai ya samu halartar mataimakin shugaban karamar hukumar, Hon. Malam Isah Mohammed, da shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Chanchaga, Malam Yusuf Muhammad Al-bashir, da majalisar kansulolin karamar hukumar, da kuma mataimaka na musamman da kansuloli masu sanya idanu a hukumomin karamar hukumar. 

No comments