Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Duk Wanda Ya Takali Ƙasarmu Za Mu Mayar Da Martani - Abiy Ahmed

Firaminitan Ethiopia, Abiy Ahmed ya sha alwashin kare ƙasarsa daga mutanen da ya kira ''masu niyyar mamaya''. Cikin wani jaw...


Firaminitan Ethiopia, Abiy Ahmed ya sha alwashin kare ƙasarsa daga mutanen da ya kira ''masu niyyar mamaya''.

Cikin wani jawabi da ya yi wa ƙasar ta gidan talbijin a bikin ranar tunawa da 'yancin kan ƙasar, Mista Abiy ya gargaɗi duk wanda ke shirin kai wa ƙasarsa hari da ya ''ƙara tunani'', yana mai cewa a shirye ƙasarsa take domin mayar da martani ga duk wanda ya takaleta.

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ciki gaba da samun ƙaruwar zaman tankiya tsakanin ƙasar da makwabciyarta Somaliya kan ɓallewar yankin Somaliland.

Rahotonni sun ce ƙasar Masar - wadda ta jima tana takun saƙa da Ethiopia kan wata madatsar ruwa a kusa da tekun Nilu - na duba yiwuwar aika dakaru zuwa Somaliya.

No comments