Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ambaliyar Ya Mamaye Yankunan Manoma 82 A Neja

Daga Awwal Umar Kontagora Ambaliyar ta mamaye makarantu da cibiyoyin lafiya 90 a cikin kwanaki biyu a Karama Hukumar Mokwa Aƙall...

Daga Awwal Umar Kontagora

Ambaliyar ta mamaye makarantu da cibiyoyin lafiya 90 a cikin kwanaki biyu a Karama Hukumar Mokwa

AÆ™alla yankunan manoma 82 ne ambaliya ta mamaye a Æ™aramar hukumar Mokwa  ta jihar Neja.

Ambaliyar ta kuma mamaye makarantu da asibitoci 90, baya ga gonaki da sauran kadarori masu yawan gaske.

Iftila’in ya faru ne bayan ruwan sama da aka tafka kamar da bakin kwarya daga ranar Litinin zuwa Talata a yankunan cikin satin nan mai karewa.

Wakilin mu ya gano cewar a gundumar Muregi kadai, mahaifar shugaban karamar hukumar, ambaliyar ta mamaye yankuna 51, ragowar 31 kuma suna gundumar Gbara.

Yunkurin ganawa da shugaban karamar hukumar, Comr. Abdullahi Muregi ya citura, a lokacin da wakilin mu ya nemi ganawa da shi a harabar hukumar N -HYPPADEC lokacin bukin kaddamar da jiragen kwale-kwale na zamani da ya gudana ranar alhamis din makon nan, bayan samun rahoton halin da yankin ke ciki.

Ambaliyar dai ya mamaye makarantu 47 da cibiyoyin lafiya a matakin farko guda 43 a yankunan Muregi, Gbara da Ja’agi da ke karamar hukumar ta Mokwa kamar yadda ma'aikatar jin kai da hukumar kula da yan gudun hijira ta jihar Neja suka tabbatar.

Daraktan yada labarai na hukumar jinkai ta jihar, Habibu Abubakar Wushishi, ya shaida  ya bada tabbacin cewar zuwa yanzu mazauna yankunan da abin ya shafa sun yi kaura zuwa wurare masu aminci.

Ma'aikatar jinkai ta jihar Neja, bisa jagorancin Hon. Ahmed Sulaiman Yumu tare da daraktan kula da sansanin yan gudun hijira, Hon. Nalango sun jajantawa al'ummomin da abin ya shafa tare da yi  masu  kira da su tashi daga wuraren da hukumar NiMet mai kula da yanayi ta yi hasashen samun ambaliya ta bayyana, wanda kuma hukumomin suka yi alkwalin bada gudunmawa gare su.

Rahotanni dai sun tabbatar ma wakilin mu cewar hukumar kula da al'ummomin da ke zaune a yankunan da ke samar da wutan lantarki na kasa ( N-HYPPADEC) na yunkurin shiga yankin dan duba irin gudunmawar da ya dace ta baiwa al'ummomin.

Karamar hukumar Mokwa dai ta dade tana fuskantar wannan matsalar a duk shekarar da aka samu yawaitar ruwan sama sakamakon zaizayar kasa da rashin magudanan ruwa, da kuma mutanen da suka zabi rayuwa kusa da ruwa sakamakon kamun kifi da noma da suke yi a yankunan gabobin ruwan.

No comments