Daga Awwal Umar Kontagora Hukumar da ke kulawa da al'ummomin da ke zaune a yanukan da ke samar da wutan lantarki ta kasa ( N -HYPPADEC) ...
Daga Awwal Umar Kontagora
Hukumar da ke kulawa da al'ummomin da ke zaune a yanukan da ke samar da wutan lantarki ta kasa ( N -HYPPADEC) ta kaddamar da jiragen ruwa na zamani ga jahohin da ke karkashin hukumar dan saukakawa al'ummomin samun safara cikin sauki.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan kammala bukin kaddamarwar a harabar shalkwatan hukumar da ke minna fadar gwamnati jihar Neja. Babban daraktan hukumar ta kasa, Alhaji Abubakar Sadiq Yelwa, yace hukumarsa ta kaddamar da wadannan jiragen ne bisa goyon bayan gwamnatin tarayya, duba da kudurin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na kyautata rayuwar al'ummar kasar nan, ta hanyar samar masu da abubuwan more rayuwa.
A jihar Neja kawai, a shekarar 2016 da hukumar tazo an samu hasarar rayuka guda talatin da shida, wanda a yau kamar yadda maigirma mataimakin gwamnan Neja, Comr. Yakubu Garba ya fadi a samu adadin hasarar rayuka sha tara kamar yadda kididdiga ya nuna, ka ga ke nan bisa matakan da hukumar mu ke dauka ana samu raguwar hadurran ruwa da ke janyo salwantar rayuka.
Yau ce ranar safarar ruwa ta duniya ( World Maritime Day) mun kaddamar da rabon jiragen ruwa ga jahohi tara cikin goma da ke karkashin hukumar mu, sannan za mu dubi sauran abinda wasu yankuna suka bukata na safara mu ba su, makusudin wadannan jiragen ruwan shi ne saukakawa al'ummomin da abin ya shafa dan gane da safara a cikin ruwa, ganin safarar ruwa na daga cikin hanyoyin safara da duniya ta amince da shi.
Dangane da yadda za a gudanar da ayyuka da jiragen kuma, jahohin da suka samu shiga shirin su zasu koma su tsara yadda za a gudanar da aikin jiragen a jahohin su. Ba mu tsaya nan ba akwai ayyuka da dama da muka gabatar a baya, kuma yanzu haka akwai wasu ayyukan da muka sanya a gaba dan kyautata rayuwar wadannan al'ummomin.
Da yake jawabi, mukaddashin gwamnan Neja, mataimakin gwamna, Comr. Yakubu Garba, ya jawo hankalin hukumar musamman kan yadda take rabon kayyakin da ya shafi al'ummomin da abin ya shafa da tafi mayar da hankali akan yankunan da abin yafi shafa.
Yace bisa kididdiga a baya an samu hadurra wadanda ya janyo hasarar rayuka da dama, wanda yanzu alkalumma na nuna cewar hadarin ruwa ya fara raguwa ainun, duk da haka akwai bukatar hukumar ta kara hada hannu da gwamnatocin jahohin da abin ya shafa wajen samar da rigunan kariya wanda yana taimakawa gaya koda hadarin jirgi ya auku ana samun sauki kai agajin gaggawa wajen ceto rayukan jama'a.
Samar da wadannan jiragen na zamani ba zai wadatar kadai ba, dole a cigaba da anfani da jiragen kwale-kwale na gargajiya duba da yanayin tattalin arzikin kasa.
Duk da haka muna yabawa hukumar N -HYPPADEC bisa kokarin da take yi lungu da sako musamman a yankunan da hukumar ta shafa. Muna bibiyar ayyukar hukumar kuma za mu cigaba da bada shawarwari a matsayin gwamnati ta yadda za a samu nasarar da ake bukata dan cigaban kasa da kyautatatwa rayuwar wadannan al'ummomin dan cin moriyar mulkin dimukuradiyya.
No comments