Rashin samar da ingantaccen tattalin arziki a cikin al'umma barazana ce ga adalci. Adalci shine tushen tsarin zamanta kewa dake kawo zam...
Rashin samar da ingantaccen tattalin arziki a cikin al'umma barazana ce ga adalci. Adalci shine tushen tsarin zamanta kewa dake kawo zaman lafiya ga dukkan al'umma. Idan al'umma ta faɗa cikin halin niʼƴasu na rashin tabbas a rayuwa komai na iya faruwa da wannan al'ummar, idan gwamnati ta kasance tana tafiya ba wanda yasan Ina ta dosa to al'umma zasu kasance cikin mawuyacin hali.
Don samar da zaman lafiya, tsaro, kwanciyar hankali ga jama'ar da Gwamnati take mulka ya kamata gwamnati ta kasance mai gaskiya da adalci. Domin babu wata hanyar da za ta kai ga ci gaba mai dorewa sai da samar da zaman lafiya da kuma adalci.
Matsalolin tattalin arzikin da muke fama da su a kasar nan, sun samo asali ne daga irin munanan manufofin da gwamnatin shugaba Tinubu ta zo mana dasu kuma take ci gaba da tafiya a kai.
Cire tallafin man fetur ba zato ba tsammani ya jefa talakawa cikin halin kunci da wahala, maimakon a duba lamarin sai ma ƙarin kudin mai da ake yi kullum ba tare da samar ma jama'a da wani hanyar rage wannan raɗaɗin ba.
‘Yan Najeriya suna cikin wani hali wanda ba sai an tsaya Dogon bayani ba, kowa yasan halin da ake ciki, musamman mu arewa, bayan wahala harma da rashin tsaro, kullum ana cikin sace mana yanuwa, ana yi wa Mata FyaÉ—e duka da sunan rashin tsaro wanda ana iya kawo kashen sa cikin lokaci kadan in ana so.
Zanga-zangar Lumana hakkinmu ne, dole ne mu yi zanga-zangar adawa da rashin shugabanci nagari da muke fama dashi. Ba za mu ci gaba da zama bayi a kasarmu ba, dole ne mu yi magana kan halin da Kasarmu ke ciki.
Matasa zamu fito kan titi a ranar 1 ga Oktoba kuma da zarar gwamnati ta kasa sauya manufofin tattalin arzikin da bala'i da ake fama dashi a wannan Kasar to zamu yi ta fita koda yaushe a dukkan jihohin Najeriya.
Comrade Yahaya M Abdullahi.
Arewa Youth Ambassadors.
24 ga Satumba, 2024
No comments