Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Aikin Mu Na Al'umma Ne, SP Ibrahim Zubairu

Daga Hassan Ibrahim SP Ibrahim Zubairu, DPO Kasuwan Mata, Divisional Police HQ, Sabon Gari, Zaria, ya ce aiki na jami'an tsaro aiki ne n...



Daga Hassan Ibrahim

SP Ibrahim Zubairu, DPO Kasuwan Mata, Divisional Police HQ, Sabon Gari, Zaria, ya ce aiki na jami'an tsaro aiki ne na al'umma wanda ya shafi kare lafiyar su da dukiyoyin su.

Ya bayyana hakan ne jim kaÉ—an bayan amsar sarautar 'ENYI OHA' daga Sarkin Iyamuran Zazzau Igwe (Sir) Vitus Ibe Unogu, Eze ndi Igbo Zazzau, wanda ya gudana a fadar Sarki da ke Graceland, Sabon Gari, Zaria.

SP Ibrahim Zubairu ya yi bayanin cewa, aiki na jami'an tsaro aiki ne na al’umma wanda ya shafi kare lafiyar su da dukiyoyin su.

“Har kullum a matsayin mu na jami'an tsaro an koya mana zamantakewa da mu'amala na zama da mutane, wanda ko mai laifi ne, za mu yi Æ™oÆ™arin jawo shi jiki  da nuna masa cewa  wannan hanyar ba mai É“ullewa É“ace, cikin kalamai na lumana da tattausan murya. Mu kan haÉ—a aikin mu da nasiha da jawo hankali kan  abubuwan da muka sani na shari'ah da al’ada a matsayin mu na mutane”, in ji shi.

Dangane da sarautar da aka bashi, SP Ibrahim Zubairu, ya nuna jin daɗin sa da godiya ga Allah (SWT) don ganin wannan rana mai matuƙar tarihi a rayuwarsa, kasancewar ba kuɗi bane ya bashi wannan abu illa hukunci ne na Allah (SWT).

“Ina zaune ne suka aiko min da takarda cewa na cancanci wani lambar yabo daga wajen su, na albishir ta wannan sarauta da aka bani a yau. A irin tsari nawa kowanne Æ™abila nawa ne, ban nuna wani banbanci wajen gudanar da aiki, daidai gwargwado muna zaune da kowa lafiya, Na kan yi Æ™oÆ™ari wajen kyautata mu'amala na da kowa”, In ji shi.

Ga abokanan aiki, SP Zubairu yace  babu abin da zance musu sai godiya, kasancewar na yarda da mataimaka a duk inda na sami kaina wajen aiki.

Ibrahim ya kuma ƙara da cewa na kan yi yadda zan jawo su a jikina dan tabbatar da tsaro da oda a duk inda na sami kaina yayin aiki.

Tun farko a jawabinsa, Sarkin Iyamuran Zazzau, Eze ndi Igbo Zazzau, Igwe (Sir) Vitus Ibe Unogu, ya ce SP Ibrahim Zubairu ya kasance mai kyautatawa a gare su, a don haka za mu ba shi wannan sarautar na 'ENYI OHA' wato abokin kowa.

Iyalai, ƴan uwa da abokanan arziƙi, sun shaida wannan sarauta da aka ba SP Ibrahim Zubairu tare da nuna farin cikinsu da kuma yi masa fatan alkhairi a ɗaukacin rayuwar sa baki ɗaya.


No comments