Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Maulud: Da Shugabanni Za Su Koyi Darussan Adalci Da Tausayin Manzon Allah Duk Wasu Kurakuran Da Ake Samu Za Su Kau – In ji Maidala'ilu

Daga Awwal Umar Kontagora An bayyana cewar ware rana dan yin hutun mauludu da gwamnati ke yi abin a yaba ne, saboda nuna muhimmancin wannan ...


Daga Awwal Umar Kontagora

An bayyana cewar ware rana dan yin hutun mauludu da gwamnati ke yi abin a yaba ne, saboda nuna muhimmancin wannan ranar, amma da gwamnati za ta dauki shiri na musamman dan zama da masana su bayyana irin falala da koyar da shugabanni irin adalci da tausayin manzon Allah ga al'umma ya zama shugabannin su dauki darussan kuma sun aiwatar da shi, da kurakuran da ake samu na zarmiya da satar dukiyar gwamnati da sun kau. Babban limamin masallacin juma'ar Tunga da ke minna, Sheikh Muhammad Salisu Maidala'ilu ya bayyana haka a lokacin da yake tsokaci kan mauludin manzon Allah da ke gudana a halin yanzu.

Maidala'ilu, ya cigaba da cewar yadda ake gudanar da bukin mauludin ya bambanta bisa fahimta da shaukin soyayya ga manzon Allah a wannan watan, wasu na shirya taruka dan karantar da darussan rayuwar manzon Allah, wasu kuma kan shirya bukukuwan cin abinci da iyalai, yayin da wasu suka dauka yawauta karanta Alqur'ani mai tsalki a wannan lokacin, wanda shi karanta Alqur'ani shi ne mafi muhimmanci kuma duk abinda za ka aiwatar muddin bai sabawa karantarwar addini ba daidai ne.

Malamin, ya cigaba da cewar babban abinda aka fi bukata da musulmi shi ne nuna soyayya da shauki akan manzon Allah, wanda koda baka mauludi muddin kai musulmi ne to masoyin manzon Allah ne, bai halatta don mutum bai mauludi ba, ka Kore shi daga soyayyar manzon Allah, haka kuma bai kamata a bullo da wasu abubuwan da suka sabawa karantarwar addinin musulunci a cikin mauludi ba, domin ba a addinin musulucin da ra'ayi kuma ba a aiwatar da shi da son zuciya, wajibi ne musulmi yasan bagiren komai akan turbarsa, domin musulunci ya taho da komai, kuma Alqur'ani mai tsalki ya karantar da komai sai in binciken mutum bai kai ba.

Saboda ina jawo hankalin musulmi musamman shugabanni da su dauki wannan watan na mauludin manzon Allah da muhimmanci, su kusanci masana addinin musulunci, su san waye manzon Allah, ya yagudanar da rayuwarsa, ya ya rike amanar da aka ba shi, tabbas idan shugaba ya samu wannan ilimin kuma ya gudanar da rayuwarsa akai, tabbas zai samu mafita da gudanar jagoranci bisa amana da adalci.

Sheikh Muhammad Maidala'ilu, ya jawo hannkalin iyaye kan amanar da aka ba su na karantarwa tare da kulawa da tarbiyar yayan su, ta hanyar karantar da su Alqur'ani mai tsalki, ba su ilimin addini da na zamani da koyar da su sana'o'i domin addinin musulunci ya ta'allaka dukkanin wadannan abubuwan a cikin tarbiyar da iyaye ya kamata su dora yayansu akan shi.

Shehin, malamin ya cigaba da cewar watan mauludin manzon Allah, ba wata ba ne na nishadi dan aiwatar da duk abinda mutum ya ga dama ba, wata da ake son mutum ya natsu ya koyi darussan da ta ke dauke daga farkon rayuwar manzon Allah, har zuwa wafatinsa, yadda ya gudanar da rayuwarsa, yadda ya zauna da jama'a, yadda ya shugabanci al'umma, idan musulmi ya samu wadannan darussan kuma yayi aiki da su zai samu ribar duniya da lahirarsa.

Dukkan wadannan jarabawowin da duniya ke fuskanta a yau, ya biyo bayan watsi da karantarwar manzon Allah, idan muka tuba muka koma akan daidai, da yardar Allah dukkkan wadannan iftila'o'in zasu kau.


No comments