Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dukkanin Kwangilar Da Za A Bayar Za Mu Tabbatar An Bi Dukkanin Ka'idodin Da Suka Dace, In ji Gwamnan Jihar Kebbi

Daga Awwal Umar Kontagora Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu ya bayyana cewar gwamnatinsa za ta tabbatar dukkanin...


Daga Awwal Umar Kontagora

Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu ya bayyana cewar gwamnatinsa za ta tabbatar dukkanin aikin kwangilar da za'a bayar an bi ka'idodin da suka dace kafin a amince da su.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wurin wani taron kwanaki biyu na  baiwa jami'an gwamnati masu kula da bangaren ka'idodin bada ayyuka (procurement)/na ma'aikatun gwamnatin Jihar horo akan sanin makamar aiki wanda aka gudanar a babban dakin taron masaukin shugaban kasa wato Presidential Lodge da ke cikin garin Birnin Kebbi.

Gwamnan ya jinjinawa bangaren ofishin da ke tabbatar da bin doka wajen bayar da kwangila bisa shirya wannan babban taron da su ka yi.

Haka kuma  ya cigaba cewar gwamnatinsa za ta tabbatar da gudanar da adalci da kuma tabbatar da an gudanar ayyukan cigaban al'umma a matsayin babban abinda gwamnatinsa ta sanya a gaba.

Ya cigaba da bayyana cewar karkashin jagorancinsa a matsayin gwamnan Kebbi, zai tabbatar da cewa dukkanin ka'idodin da ya kamata a cika a wurin samun aikin gudanar da kwangila an cika su kafin sanya hannu akan yarjeniyoyin gudanar da ayyukan kwangilar.

Haka kuma yayi kira ga wadanda su kaci gajiyar horon da su tabbatar sun yi amfani da ilimin da suka samu yadda ya dace inda kuma ya bukaci ma'aikatan hukumar da su yi aiki da manyan shugabannin hukumar a lokacin da suka fuskanci wata matsala a wurin gudanar da ayyukansu.

Gwamnan ya cigaba da gudanar jawabi jindadinsa bisa kyautar karramawar da aka ba shi bisa irin ayyukan cigaban da yake gudanarwa a fadin Jihar.

Kauran Gwandu ya kara jaddada kudurinsa na fara biyan sabon mafi karancin albashi idan aka kammala dukkanin shirye-shiryen da suka dace.

Tun da farko,  da yake nasa jawabin a wurin taron, shugaban Price Intelligence and Public Procurement Bureau (Due process) Alhaji Muhammad Surajo Garba ya bayyana cewar babban makasudin taron shi ne tabbatar da ma'aikatun gwamnatin jihar sun gabatar da kasafin kudi daidai da abinda gwamnati ta ware.

Haka kuma ya bayyana cewar wannan taron shine kashin farko na ma'aikatan daga hukumomin gwamnati guda 14 inda ya bayyana kashi na biyu zai zo cikin watan Oktoba mai zuwa.

Ya yi kira ga mahalarta taron da su yi amfani da ilimin da zasu koya a wurin taron domin cigaban bangaren.

A wurin taron an bai wa gwamnan kyautar karramawar Procurement Compliance and Good Governance Award 2024 wanda 'Association of Public Procurement Practitioners of Nigeria (APPON)' ta ba shi.


No comments