Daga Awwal Umar Kontagora Kungiyar ta baiwa gwamnan Kebbi lambar na karramawa. An bada wannan lambar yabon ne a wurin wani babban taron ta n...
Daga Awwal Umar Kontagora
Kungiyar ta baiwa gwamnan Kebbi lambar na karramawa. An bada wannan lambar yabon ne a wurin wani babban taron ta na shekara-shekara a karo na 29 wato 'ANAN 29th Annual Conference' wanda aka yi wa take da 'Advancing Accounting Excellence in a Changing World".
An gudanar da taron ne a garin Abuja inda manyan mutane da dama daga fadin Nijeriya suka halarta.
Gwamnan ya samu wakilcin mataimakinsa Sanata Umar Abubakar Tafida ne a wurin taron. Mataimakin gwamnan ya samu rakiyar manyan jami'an gwamnatin Jihar a wurin taron da suka hada da shugaban ma'aikatan Jihar Kebbi, Alhaji Safiyanu Garba Bena, shugaban jam'iyyar APC na jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Kana Zuru, kwamishinoni da manyan masu baiwa gwamna shawara da kuma babban akawun Jihar Kebbi, Alhaji Ibrahim Nahalidu da dai sauransu.
Kungiyar ta bai wa gwamna wannan lambar yabon ne bisa irin kokarinsa wajen cigaban aikin gwamnati da kuma irin gudunmawa da taimakon da yake yiwa wannan kungiyar da kuma irin kokarin kwatanta adalci a ayyukansa a matsayinsa na gwamnan Jihar Kebbi.
Da yake karbar lambar yabon, a madadin gwamnan, Mataimakin gwamnan yayi godiya ta musamman ga kungiyar inda kuma ya kara jaddada cewar gwamnatin Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu, za ta cigaba da baiwa kungiyar dukkanin irin goyon baya da taimakon da take bukata.
Haka kuma ya bayyana cewar gwamnatin Kebbi karkashin jagorancin Dakta Nasir Idris Ƙauran Gwandu za ta cigaba da gudanar ayyukan cigaban al'ummar jihar Kebbi bisa doka da kuma adalci tare da sarrafa dukiyar al'ummar Jihar bisa adalci ga kowa domin cigaban Jihar baki daya.
No comments