Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnan Kebbi Ya Yabawa Hukumar NEMA Kan Bayar Da Tallafi Ga Wadanda Ibtila'in Ambaliyar Ruwa Ya Shafa

Daga Awwal Umar Kontagora Gwamnan Jihar Kebbi, Dr. Nasiru Kauran Gwandu ya yabawa hukumar bayar da agajin gaggawa da tallafin jinkai ta (NEM...

Daga Awwal Umar Kontagora

Gwamnan Jihar Kebbi, Dr. Nasiru Kauran Gwandu ya yabawa hukumar bayar da agajin gaggawa da tallafin jinkai ta (NEMA) bisa irin yadda suke gudanar da ayyukansu a jihar wajen gano wuraren da ambaliyar ruwa ko wani ibtila'i ya shafa domin bayar da agajin gaggawa cikin lokaci:

Gwamnan yayi wannan yabon ne a lokacin wani babban taron da ya gudana a garin Birnin Kebbi ranar Alhamis din makon da ya gabata akan duba yanayin wuraren da zasu iya fuskantar matsalar ambaliyar ruwan bana a jihar wanda aka yiwa take da " 2024 Downscaling of Flood Early Warning Strategies of Early Actions" a turance.

Gwamnan ya samu wakilcin mataimakinsa Sanata Umar Abubakar Tafida ne a wurin taron.

Da yake jawabi a wurin taron, wakilin gwamnan a wurin taron, Sanata Umar Abubakar Tafida ya bayyanawa mahalarta taron cewar ilimi da basirar da Allah ya ba su a wannan bangaren zai taimaka wajen bayar da shawarwarin da ya dace wajen magance matsalolin ambaliyar ruwan da kuma tseratar da rayuka da dukiyoyin al'umma.

Haka kuma ya bayyana cewar a wannan shekarar a halin yanzu jihar Kebbi ta fuskanci matsalar ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 13 inda yayi sanadiyar tayar da wasu al'ummomi daga kauyukansu da kuma lalata dukiyoyi har ma da amfanin gonaki.

Saboda haka wannan taron zai taimaka wajen gano wuraren da suke fuskantar barazanar ambaliyar ruwa a bana domin daukar dukkanin matakan da suka dace wajen dakile wannan barazanar ta ambaliyar ruwan.

Haka kuma ya kara da cewar gwamnatin jiha a shirye take ta baiwa hukumar NEMA dukkanin gudummawar da take bukata wajen magance irin wadannan matsalolin.

Ita ma shugabar hukumar ta NEMA ta kasa Hajiya Zubaida Umar da take na ta jawabin, ta bayyana cewar yanzu haka mutane sama da miliyan daya ne (1,061,254) matsalar ambaliyar ruwa ta shafa a Nijeriya inda sama da mutane dubu dari shida (634,035) suka rasa muhallansu kuma gidaje sama da dubu casa'in (94,741) suka rushe duk a fadin Nijeriya.

Daraktan magance faruwar ibtila'i wato " Director Disaster Management" na hukumar NEMA Dakta Daniel Obot ne ya wakilci shugabar hukumar ta kasa a wurin taron.

Daraktan ya kara da cewar akalla kananan hukumomi goma sha shida (16) na jihar Kebbi ne suke fuskantar barazanar ambaliyar ruwa a bana.

Haka kuma ya bayyana cewar babban makasudin irin wannan taron shi ne duba wuraren da suke fuskantar hadarin ambaliyar ruwa domin daukar matakan da suka dace da suka hada da sanar da al'umma da kuma wayar musu da kai a kan wannan dama dukkanin wani matakin da ya dace.

No comments