Daga Awwal Umar Kontagora Babban daraktan hukumar kula da al'ummomin da ke zaune yankunan da ke samar da wutan lantarki ta kara ( N-HYPP...
Daga Awwal Umar Kontagora
Babban daraktan hukumar kula da al'ummomin da ke zaune yankunan da ke samar da wutan lantarki ta kara ( N-HYPPADEC), Abubakar Sadiq Yelwa, ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu akan tsare tsare da matakan da yake dauka akan ambaliyar ruwan sama ta hanyar daukar matakan da suka dace wajen ganin an kawar da barnar da ambaliyar kan janyo da kyautatawa wadanda abin ya rutsa da su.
Yelwa, ya cigaba da cewar gwamnatin tarayya ta hannun hukumominta tana aiki ba dare ba rana wajen ganin yankunan da ambaliyar ruwan sama ya shafa da matsalolin da kan biyo baya ta ilmantar da su ta hanyar wayar masu da kai dan tsaron rayuka da dukiyoyi.
Ya cigaba da cewar matakan da ake dauka ya nuna karara cewar gwamnatin tarayya ta damu ainun akan matsalolin da suka shafi yankunan da jama'a ke zama, musamman ganin yadda ta himmantu wajen ayyukan raya kasa da take aiwatarwa a kasar nan.
Ya bayyana cewar hukumarsa ta himmantu wajen wayar da kai, da ilmantar da al'ummomin da ta kirkira, tare da sanya idanu akan bukatun gaggawa da abinda ake tsammanin faruwarsa a gaba akan ambaliyar ruwan sama da wasu matsalolin na daban.
Yelwa, yayi bayanin hakan be lokacin da karin haske ga wasu jama'a da aka horar a Abuja fadar gwamnatin tarayya. akan nazarin ruwan sama na hukumar na shekarar 2024, yace akai bukatar nazari da bincike akan yankuna ga dukkanin bangaren hukumar na jahohi.
Ya ce, bukatar yin nazarin yana daga cikin ayyukan hukumar, na tsara yadda ayyuka zasu gudana da shirye shirye akan tsari da yankuna ke bukata.
Ya nuna yakininsa akan ayyukan shekarar 2024 zasu samar da sakamakon da ake bukata wajen tsari da tabbatar da ayyuka, da shirye shirye fiye da na baya saboda jami'an hukumar da suka samu kwarewa akan shirin zasu gabatar da su.
Babban daraktan, ya yabawa hukumar gudanarwar hukumar da masu bada gudunmawa da masu halarta saboda sha'awarsu ga shirin da lokutan su a lokacin gabatar da shirin.
No comments