Daga Awwal Umar Kontagora Gwamnan Jihar Kebbi Kwamared Dakta Nasir Idris Ƙauran Gwandu ya Jagoranci wata babbar tawaga daga Jiha...
Daga Awwal Umar Kontagora
Gwamnan Jihar Kebbi Kwamared Dakta Nasir Idris Ƙauran Gwandu ya Jagoranci wata babbar tawaga daga Jihar Kebbi zuwa wani babban taron duniya na 79th UNGA Side Event
Taron yana gudana ne a Birnin New York dake kasar Amurika. Anyi wa taron suna da 79th UNGA Side Event High-level Global Executive Sustainable Investments Grands and intervention.
Taron zai baiwa jihar Kebbi damar gabatar da hanyoyin da jihar Kebbi za ta tallata irin hanyoyin da wasu zasu iya sanya hannun jari da kuma huldodin kasuwanci.
Daga cikin tawagar Gwamna a wurin wannan gagarumin taron akwai Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi Alhaji Yakubu Bala Tafida, Kwamishinan kananan hukumomi da masarautun jihar Kebbi Honorabul Garba Umar Abubakar Dutsinmari, Kwamishinan harkokin kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arzikin jihar Kebbi Honorabul Abba Sani Kalgo Kwamishinan Shari'a Junaid Marshall dadai sauransu.
Taron ya baiwa Jihar Kebbi damar tallata irin baiwar da Allah yayiwa jihar na albarkatun kasa da yadda za'a samu masu saka hannun jari a jihar.
Wannan tafiyar domin halartar wannan taron zai kara baiwa gwamnatin jihar damar bude kofofinta na hulda da wasu kasashen da dama ta yadda jihar za ta amfana.
No comments