Daga Awwal Umar Kontagora Gwamnan Kebbi Kwamared Dakta Nasir Idris Ƙauran Gwandu, ya yi kira ga al'ummar Musulmi da su yi am...
Daga Awwal Umar Kontagora
Gwamnan Kebbi Kwamared Dakta Nasir Idris Ƙauran Gwandu, ya yi kira ga al'ummar Musulmi da su yi amfani da dukkanin damar da suka samu wajen yada addinin musulunci.
Gwamnan yayi wannan kiran ne a wurin taron Kaddamar da wani littafi da wani sanannen malamin addinin musulunci Sheikh Dakta Turkiy Ibn Salih Almaiman ya rubuta.
An yi taron Kaddamar da littafin ne a garin Sakkwato dake Jihar Sakkwato. A wurin taron. Gwamna Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu ya bayar da da gudummawar naira miliyan uku inda Uwargidansa Hajiya Zainab Nasare Nasir Idris Kauran Gwandu ta bayar da gudummawar naira miliyan biyu.
Shi dai wannan littafin Malam Bello Abubakar Nassarawa Birnin Kebbi ne ya fassara shi zuwa Hausa inda aka ba shi suna da "Addu'a Takobin Mumini"
Mai baiwa gwamna shawara akan harkokin addinin musulunci Injiniya Imrana Usman ne ya wakilci gwamna Kwamared Dakta Dr Nasir Idris Kauran Gwandu a taron.
A lokacin da yake jawabi a wurin taron, wakilin gwamnan, ya bayyana cewar maigirma gwamna bai samu halartar taron ba ne sanadiyyar wata tafiya da yayi zuwa kasar waje domin gudanar da wasu muhimman ayyuka.
Haka kuma ya bayyana cewar Gwamna Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu a shirye yake a koda yaushe wajen taimakawa harkokin yada addinin musulunci a koda yaushe.
Wakilan Gwamnan, yayi amfani da wannan damar wajen bayyana irin ayyukan da maigirma gwamnan ya gudanar a bangaren cigaban addinin musulunci da suka hada da gyara da gina sabbin masallatai, bayar da tallafin yada addinin musulunci da dai sauransu.
Haka kuma gwamnan yayi godiya da Jinjina ga Sheikh Ibrahim Mansur Sakkwato wanda shi ne ya taimakawa wanda ya fassara littafin Malam Bello Abubakar Nassarawa Birnin Kebbi wajen fassara littafin.
Ita ma uwargidan Glgwamnan, Hajiya Zainab Nasare Nasir Idris Kauran Gwandu da take nata jawabin a wurin taron ta bakin wakilinta a wurin taron Malam Abdulrasheed, shugaban Gidauniyar Nasara Foundation ta bayyana cewar uwargidan gwamnan ta bayar da nata gudunmawar ta naira miliyan biyu.
Kwamishinan harkokin Addinin Musulunci na jihar Sakkwato, Sheikh Dakta Jabir Sani Maihulla ne ya wakilci gwamnan Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu, a wurin taron inda Sheikh Mansur Ibrahim Sakkwato ya wakilci mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III.
No comments