Daga Awwal Umar Kontagora Gwamnatin Jihar Kebbi ta biya Naira miliyan dari tara da hamsin (₦950m) kudin Jarabawar WAEC da NECO g...
Daga Awwal Umar Kontagora
Gwamnatin Jihar Kebbi ta biya Naira miliyan dari tara da hamsin (₦950m) kudin Jarabawar WAEC da NECO ga yara yan asalin Jihar Kebbi wanda makarantar Key Science Academy, Masaka Abuja ta rike sanadiyyar kasa biyan kudin Jarabawar:
Daliban da aka biyawa kudin dai su dari da sittin da hudu (164) wadanda dukkaninsu yan asalin Jihar Kebbi ne.
Makarantar dai ta rike sakamakon jarabawar daliban ne saboda kasa biyan kudin Jarabawar wanda gwamnatin Jihar da ta gabata ta kasa biya, inda yanzu wannan gwamnatin karkashin jagorancin gwamna Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu ta biya kuma ta karbo musu sakamakon jarabawarsu.
Kwamishiniyar harkokin ilimi a matakin farko wato " Basic and secondary Education" Dakta Halimatu Muhammad Bande ce ta bayyana sanarwar biyan kudin tare da karbo sakamakon ranar alhamis din da ta gabata a garin Birnin Kebbi a lokacin da taron baiwa daliban sakamakon jarabawar tasu wanda mataimakin gwamnan Jihar Kebbi Sanata Umar Abubakar Tafida ya jagoranta.
Da take jawabi a wurin taron, Dakta Halimatu Muhammad Bande ta bayyana cewar da yawan yaran suna da burin karatun likita da sauran bangarorin kimiya da kiwon lafiya amma sanadiyyar rashin sakamakon jarabawar sun kasa cin ma wannan burin nasu amma yanzu gwamna Kwamared Dakta Nasir Idris Ƙauran Gwandu ya biya kudin Jarabawar tasu domin su sami damar cigaba da karatu domin cin ma burinsu.
A nasa jawabin, mataimakin gwamnan, Sanata Umar Abubakar Tafida wanda ya jagoranci bayar da sakamakon jarabawar, da yake nasa jawabin a wurin taron ya bayyana cewar wannan gwamnatin karkashin jagorancin Kwamared Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu a shirye take a koda yaushe wajen tallafawa harkokin ilimi ta kowani bangare.
Haka kuma ya kara da cewar gwamna kwararren malamin makaranta ne wanda ya san muhimmancin ilimi a matsayin kashin bayan cigaban al'umma saboda baya wasa da harkokin ilimi kuma zai cigaba da bayar da da dukkanin gudummawar da ta dace ga harkokin ilimi a fadin Jihar.
Haka kuma ya kara da godiya ta musamman ga maigirma gwamna bisa biyan wannan kudin da kuma karbo sakamakon jarabawar yaran domin ba su damar cigaba da karatun su inda ya kara jinjinawa gwamna bisa kokarin sa a harkokin ilimi.
Daga karshe mataimakin gwamnan yayi kira ga daliban da su mai da hankali wajen karatu sosai kuma su sakawa maigirma gwamna da alheri bisa wannan karramawar da yayi musu ta hanyar mai da hankali a karatunsu.
Shi ma da yake jawabi godiya a madadin daliban, Aminu Ahmad Kadanho yayi godiya ta musamman ga gwamna bisa wannan biyan kudin da kuma karbo sakamakon jarabawar daliban wanda hakan zai ba su damar cigaba da karatunsu.
Daga karshe mataimakin gwamnan ya jagoranci mika sakamakon jarabawar ta WAEC da NECO ga daliban tare da taimakon kwamishiniyar harkokin ilimi Dakta Halimatu Muhammad Bande.
No comments